Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas
Published: January 19, 2026 at 11:43 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jama’a sun yi tururuwa suna dibar ganimar man dizel yayin da tankar mai ta faɗi a Legas

Tanka mai ɗauke da dizal ta kife a gadar Tincan Liverpool da ke yankin Apapa a jihar Legas, inda wasu mazauna unguwa da masu wucewa suka rika kwashe man da ya zube.

Lamarin ya faru da safiyar yau Litinin kuma Shaidun gani da ido sun ce jami’an kula da zirga-zirga ba su kai wurin nan take ba.

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta ce an rufe gadar na ɗan lokaci, amma daga baya an sake buɗe ta bayan jami’an kashe gobara sun rage haɗarin man da ya zube.

Hukumar ta ƙara da cewa zirga-zirga ya inganta yayin da ake jiran motar ɗaukar tankar.

Hukumar ta kuma gargadi jama’a kan haɗarin irin wannan hali, tana tunatar da mummunan sakamakon da ya faru a baya a sassan ƙasar, inda mutane da dama suka rasa rayukansu yayin ƙoƙarin kwashe mai daga tankoki da suka kife.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba
Next Post: Sojin Saman Najeriya Sunyi Gagarumar Nasara A Yankin Borno

Karin Labarai Masu Alaka

Suvr Jahun: Ya Kamata Obasanjo Ya Bar Al’umar Ƙasa Su Fito Da Wadda Suke So 2027 Najeriya
Amurka Ta Kai Hari Kan ‘Yan ISISI A Jihar Sakkwato Bisa Rokon Gwamnatin Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Hikima Da Jagorancin Sarkin Gombe A Shekaru 12 Na Jagoranci Afrika
Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
  • Shugabannin Kasashen Afirka Ta Tsakiya Sun Kamallah Taron Koli Afrika
  • Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai Afrika
  • An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
  • NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Afrika
  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika
  • Jami’in Diflomasiyyar Da Ake Zargi Da Kisan Prime minister Ya Daukaka Kara Afrika
  • Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.