Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya
Published: November 21, 2025 at 4:43 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Shugaban Hukumar Wasannin Harbi (Shooting Sport) ta Najeriya, Mohammed Shettima, yana neman hadin gwiwa da masu shirya gasar Olympics ta matasa ta Dakar 2026 don bunkasa wasannin Harbi a Najeriya.

A ziyarar da ya kai kwanan nan zuwa Kwamitin Shirya Wasannin Olympics na matasa na Dakar 2026, a Senegal, Shettima, ya samu kyakyawan tarba daga Babbar Daraktar Hulda da Jama’a ta wasanni Madam Fanta Diallo, bangarorin biyu sun tattauna fannoni masu amfani don inganta hadin gwiwa mai zurfi, musamman a fannin bunkasa Wasannin Harbi.

Shugaban NSSF wanda ya hau mulki a ranar 25 ga Satumba, 2025, ya shaida wa wakilin Kwamitin shirya wasannin Olympics na Dakar cewa Najeriya tana da damammaki da yawa a wasanni, musamman a wasannin Harbi, don bunkasa muhimman abubuwan da suka faru a duniya, ya kara da cewa hadin gwiwar zai bude hanyar zuwa ga kwarewar wasanni ta Afirka a fagen wasanni na duniya.

Da take jawabi Madam Fanta ta yi alƙawarin yin aiki kafada da kafada da NSSF da kuma Kwamitin Olympics na Najeriya don cimma fa’idodin juna.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/RAHOTON-WASANNI-SAFE-21-11-2025.mp3
Wasanni

Post navigation

Previous Post: Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20
Next Post: Nnamdi Kanu Zai Daukaka Kara Har Zuwa Kotun Koli

Karin Labarai Masu Alaka

Onana Ba Ya Cikin Tawagar Kamaru (AFCON) Wasanni
Lawal, Filin Wasa Na Rashidi Yekini Ko Turai Iyaka Wasanni
Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot. Wasanni
Sabon Jadawalin Gasar Kwalon Kafa Ta Turai 2026 Wasanni
Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025. Wasanni
CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
  • An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka
  • Duniyar Dambe A Makon Jiya Nishadi
  • Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
  • A Kowacce Rana Kasar China Tana Sayan Danyen Mai Ganga Dubu 600 Daga Kasar Venezuela Amurka
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
  • An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.