Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka
Published: February 3, 2026 at 10:21 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masar ta jibge gogaggun jiragen yaki da basu da matuka da aka fi sani da drones da turanci, daga Turkiyya a wani karamin tashar jirgin sama mai nesa daga kan iyakarta kudu maso yammacin kasar, mataki da yake nuna ana zafafa yakin basasar da ake yi a Sudan, wadda ke nuna cewa makwabciyar Sudan din tana kara shiga cikin rikicin, kamar yadda jami’ai fiye da 10 da masu fashin baki suka fada.

Masar wacce baya ga kogin Nilu da ya hadata da Sudan, tana da iyaka fiye da tsawon kilomita dubu daya da dari biyu da Sudan, tana bada cikakken goyon baya ga sojojin Sudan masu mulkin kasar, a fafatawa da take yi da dakarun wucin gadin kasar da ake kira RSF a takaice.

Masar ta fara sauya matsayarta game da rikicin na Sudan, lokacin da ‘yan tawayen na RSF suka fara samun nasaran kama wurare a yankin Darfur, da suka hada da kama birnin al-Fashir cikin watan Oktoba, inda nan ne wuri na karshe da sojojin Sudan suke da sansani.

A cikin watan Disamba ne Masar tayi gargadin cewa tsaron kasar yana da nasaba sosai da na Sudan. Kuma Masar ba zata amince da duk wani yunkuri da zai kassara diyaucin Sudan ba.

Afrika, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Mabiya Addinin Kirista Da ‘Yan Bindiga Suka Sace Sun Kubuta
Next Post: Ambaliyar Ruwa Ya Tilastawa Dubban Jama’a Rasa Muhallensu A Morocco

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
Kotun Tarayya Tabada Belin Nasiru El Rufai Afrika
Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Ta Bukaci Rwanda Ta Daina Marawa ‘Yan Tawayen M23 Baya Afrika
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika
  • Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli Afrika
  • Ganduje: Mun Janye Shirin Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Najeriya
  • ‘Yan Tawayen Houthi Sunkai Hari Isra’ila Afrika
  • Yawan wadanda suka mutu a mummunan harin yanbindiga a Jihar kwaran Najeriya yakai 170 Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.