Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya
Published: February 17, 2026 at 11:13 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar Litinin ministan harkokin wajen Iran ya gana da shugaban hukumar kayyade makaman Nukiliya na MDD, gabanin zaman shawarwari tsakanin hukumomi dake Washington da kuma Tehran, da zimmar warware takaddamakan shirin Nukiliyar Iran, da alamun babu bangare da yake nuna sassauci, yayinda Amurka take barazanar daukar matakin Soja kan Farisa.

Amurka wacce tare da Isra’la suka kai hare hare na hadin guiwa kan Iran a cikin watan Yunin bara, ta tura wani babban jirgin ruwa mai dakon jiragen yaki na sama, wanda shine na biyu zuwa gabas ta tsakiya baya ga wasu jiragen ruwan yaki da tuni suke can, a yayinda ake zaman kallon hadarin-kaji tsakanin kasashen biyu.

Wani lamari da ya kara zaman dar dar shine ganin Iran ta fara rawar daji a mashigan ruwan Hormuz, wata muhimmiyar mashigar  ruwa na kasa da kasa mai muhimmancin gaske ga kasashen larabawa da suke yankin Gulf, wadanda suka nemi a bi hanyoyin difilomasiyya wajen warware takaddamar.

A farkon watan nan ne Amurka da Iran suka sake farfado da shawarwari tsakanin su da nufin warware rikici kan shirin Nukiliyar Iran, wadda Washington da kawayenta a turai suke zargin na kera makamai ne, yayinda Iran kuma ta dage shirin ta na farar hula ne.

Afrika, Amurka, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka
Next Post: Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba

Karin Labarai Masu Alaka

Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi Labarai
Rundunar Operation Endurance Peace Ta Gano Wajen Kera Makamai A Jihar Filato Afrika
Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika
Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
Gaza Ga Albarusai Ga Yunwa Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu A Kasar Uganda Ta Bada Belin ‘Yar Gwagwarmaya Afrika
  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka Afrika
  • Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
  • Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya
  • Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa Labarai
  • Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya
  • PDP Zata Karbi Mulki 2027 Inji Shugabannin Jam’iyar Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.