Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi
Published: February 17, 2026 at 12:25 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gabanin shigowar watan azumin Ramadan, Church of Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Sabon Tasha a Kaduna ta raba kayan abinci ga Musulmi sama da 1,000, makarantun Islamiyya na Tsangaya da kuma wasu ‘yan gudun hijira (IDPs), a wani mataki da ke ƙara ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

An gudanar da rabon kayan ne a harabar Kano Road Central Mosque, inda Babban Faston Majami’ar, Dr. Yohanna Buru, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce bunƙasa haɗin kai, juriya da zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, tsawon shekaru 20 da suka gabata, Majami’ar na tallafa wa Musulmi marasa galihu da makarantun Tsangaya a jihohin Arewa biyar da kayan abinci a duk lokacin Ramadan, domin ba su damar gudanar da azumi da ibada cikin walwala.

Ya ce ana raba shinkafa, masara da sauran kayan masarufi, tare da tabarmi da butocin roba, tare da ƙarfafa wa waɗanda suka amfana da tallafin gwiwar yin addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ƙasa.

Fasto Buru ya kuma bayyana cewa, sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki, ya tattara fastoci da limamai 50 domin gudanar da gangamin kwanaki bakwai tare da ‘yan kasuwa a kasuwanni, da nufin rage farashin kayan abinci domin sauƙaƙa wa al’umma a lokacin Ramadan.

Ya ƙara da cewa kowace shekara Majami’ar na taimakawa wajen biyan belin wasu fursunonin Musulmi, domin su samu damar yin azumi tare da iyalansu.

Haka kuma ya yaba da gudummawar da wata baiwar Allah Musulma, Hajiya Ramatu Tijjani, ke bayarwa duk shekara ga zawarawa da marayu a lokutan bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Babban Faston ya yi wa Musulmi a faɗin duniya fatan samun Ramadan mai albarka, tare da kira gare su da su ci gaba da yin addu’o’i domin dorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Da yake karɓar kayan a madadin masu buƙata ta musamman, Shugaban Ƙungiyar Masu bukata ta musamman a jihar Kaduna, Malam Hassan Lawal, ya bayyana matuƙar godiya bisa wannan tallafi, yana mai kira ga attajiran Musulmi da su ƙara zage damtse wajen tallafa wa marasa galihu da kayan abinci domin su samu damar mayar da hankali ga ibada.

Haka zalika, Shugaban Ƙungiyar Makafi ta Jihar Kaduna, Malam Tukur Zubairu, ya yaba da yadda ake tunawa da su tsawon shekaru 20 a kowane watan Ramadan, yana mai cewa Allah ne kaɗai zai saka wa Faston bisa wannan karamci da kulawa.

A nasa jawabin, Imam Ibrahim Musa, wanda ya yi magana a madadin makarantun Tsangaya a Kaduna, ya gode wa Fasto Yohanna Buru bisa wannan tallafi, tare da kira ga sauran masu hali da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali na zaman tare cikin lumana.

Shi ma Murshidin Jama’atu Nasril Islam, Imam Ilyasu, ya bayyana wannan mataki a matsayin gagarumin abin a yaba, yana mai kira ga masu hannu da shuni da su riƙa fitar da zakka da sauran sadaka domin tallafawa Musulmi marasa galihu, musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba
Next Post: Gwamnatin Bola Tinubu Ta Raba Taraktoci Dubu Biyu Domin Inganta Noma

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
An Bude Makarantu A Najeriya Najeriya
‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kamfanin Magani Na Aspen Yayi Gagarumar Asara A Cinikayya Afrika
  • Shugaban Hukumar NAHCON Ya Ajeye Mukaminsa Labarai
  • Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika
  • Iran: Za A Gudanar Da Jana’izar Khamenei Bayan Kwanaki Goma Na Muharram Afrika
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Daruruwan Mutane A Afirka Ta Kudu Afrika
  • Akwai Bukatar Bincikar Umurnin Da Sakataren Tsaro Pete Ya Bada Amurka
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
  • Pakistan Zata Karbi Tattaunawar Rikicin Gabas Ta Tsakiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.