Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Fara Azumin Watan Ramadan A Najeriya Da Sassan Duniya 
Published: February 18, 2026 at 3:56 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

An Fara Azumin Watan Ramadana Na Bana a Najeriya Da Sassan Duniya

A Larabar nan 18 ga watan Febrairu 2026 a ka fara azumin watan Ramadana a Najeriya, Saudiyya da kasashen musulmi da dama.

Wannan ya biyo bayan ganin jinjirin watan Ramadana yayin da watan Sha’aban yayi kwana 29.

Wannan Shekarar Shehun Borno Alhaji Garbai Umar Elkenemi ke sanarda ganin watan a madadin mai alfarma Sarkin musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar wanda rahotanni su ka bayyana cewa ba ya kasa.

Wannan shi ne kusan karo na farko a tarihin shekarun nan da Shehun Borno ke ba da sanarwar kuma dama shi ne mataimakin shugaban majalisar sarakuna na Arewa.

Garbai Elkenemi ya bukaci musulmi su yi amfani da damar wajen yi wa shugabanni da kasa addu’ar alheri.

Malamai na kira ga masu hannu da shuni da ma ‘yan kasuwa su sa tallafi ko rangwame a farashin kayan masarufi.

Sheikh Abdullahi Bala Lau babban malami ne na sunnah a Najeriya wanda ya nuna muhimmancin rangwame a watan azumi.

Hakika musulmi kan yi amfani da watan na azumi wajen ninka kwazo a ibada da yin dogayen sallolin nafila.

Tuni majalisun tafsiri sun fara gabatarda zama inda bana Khalifan Shehu Dahiru Bauchi wato Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya bude tafsirin Shehi wanda Allah ya yi wa rasuwa a kwanakin baya. Shehu kan gudanar da tafsirin a Kaduna a tsawon shekaru masu yawa.

Izala kadai ta tura fiye da malamai 2000 a ciki da wajen Najeriya don gabatarda tafsiri.

Ga Cikekken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/02/RAMADAN-FAST-2026-HIJRA-1447-COMMENCES.mp3
Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Rediyo, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Kamfanin Dangote Zai Sayo Na’urori Daga Kasar China
Next Post: Musulmai A Kasashen Duniya Da Dama Sunfara Azumin Ramadan

Karin Labarai Masu Alaka

Zamu Tarwatsa Cibiyoyin Makamashi Da Cibiyoyin Mai Din Iran Amurka
Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama Afrika
Kudin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 10 Cikin 100 Afrika
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Gwamnatin Sojan Burkina Faso Ta Soke Jam’iyyun Siyasar Kasar Afrika
  • CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika
  • Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
  • Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran Afrika
  • An Ga Watan Ramadan A Najeriya Da Nijar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.