Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan
Published: February 20, 2026 at 1:02 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Amurka Donald Trump, ya fadawa taron farko na kwamitin wanzar da zaman lafiya da ya kafa a ranar Alhamis cewa, kasashe da suke cikin kwamitin sun bada gudumawar kudi dala bilyan bakwai 7, domin sake gine Gaza da zarar Hamas ta kwance damara, burin na ajiya makamai tabbatarsa zai yi wuyan gaske.

Tilas ta Hamas ta ajiye makamanta da janyewar sojojin Isra’ila daga zirin, yawan kudaden da aka tara domin aikin sake gine zirin, da tura kayan agaji ga mazauna yankin da yakin ya daidaita su, sune batutuwa da za su zamo zakaran gwajin dafi na tasirin wannan kwamiti.

A jawabinsa mai tsawo, shugaba Trump ya sanar da wakilan kasashe 47 da suka halarci zaman kwamitin cewa, Amurka zata bada gudumawar kudi dala bilyan 10 ga ayyukan kwamitin wanzar da zaman lafiyan.

Shugaban na Amurka yace kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA zata tara kudi dala milyan 75 domin raya kwallon kafa a Gaza, yayinda MDD zata bada gudunmawar dala bilyan biyu domin ayyukan raya al’uma.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Amurka Ta Kakaba Takunkumi Ga Kwamandojin Yakin Kasar Sudan
Next Post: Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Zata Tantance Fararen Fata ‘Yan Afirka Ta Kudu Afrika
Shugaban Trump: Washington Zatayi Cinikayya Da Indiya Amurka
Shugaba Trump Yace Tehran Tana Neman Kulla Alaka Da Washington Amurka
Shugaban Amurka Yayi Barazanar Kulle Wani Dan Jarida Amurka
Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ministan Kudin Najeriya: Bamu Samu Kudaden Da Muke Tsammani A Wannan Shekarar Ba Najeriya
  • An Tsaurara Tsaro Yayin Da Tehran Ke Shirin Karɓar Masu Jimamin Ayatollah Khamenei Afrika
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
  • Arsenal Ta Fara Kare Kambun Gasar Premier League Da Ci 3-0 A Kan Coventry City Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.