Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yaki Da Akeyi Tsakanin Isra’ila Da Amurka
Published: March 2, 2026 at 7:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yakin da Isar’ila da Amurka suke fafatawa da kasar Iran ya ci gaba ya kara tsamari a ranar Litinin, kuma ba’a ga alamar karshen sa ba. Isra’ila ta kaiwa kasar Lebanon hari, tana mai da martani ga harin da kungiyar Hezbollah suka kai mata.

Ita kuwa fadar Tehran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki na drone zuwa kasashen tekun fasha, da filin sansanin sojin sama na Bahrain, har can zuwa kasar Cyprus.

Kasar Kuwait kuwa ta harbo jiragen yakin Amurka bisa kuskure, dukkanin mutane 6 na cikin jiragen sun tsira da ran su. Wani hoton bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yarda da sahihancin sa ya nuna daya daga cikin jiragen yana yin kasa yayin da injin sa ke kamawa da wuta.

Har ila yau Amurkan ta ce Sojojin ta 4 sun mutu, amma bata bada bayanin ta yadda suka rasa rayukan nasu ba. Wasu jami’an Amurka su biyu sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutane 3 na farko da suka rasu an kashe su ne a sansanin soji a Kuwait.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da kira ga ‘yan kasar Iran da su tashi su hambarar da shugabannin su, kuma ya ce harin da ake kaiwa zai iya shafe makonni. Su kuma shugabanni addini na Iran basu nuna wata alama ta yada Makamai ba.

Wani malamin makaranta a Iran Morteza Sedighi da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho ya ce harin Amurka da Isra’ila yana kakkashe yara, kuma suna kai hari asibitoci, yace wannan shine demokradiyar da Trump yake so ya kawo mana. Farko hukumomin Iran sun kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, yanzu kuma Isra’ila da Amurka na kashe mutane inji shi.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci
Next Post: Farashin Kasuwar Yawon Bude Ido A Kasuwar Hannayen Jari Ya Fadi

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola Afrika
Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
An Gargaɗi Mazauna Maiduguri Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya Afrika
Ana Tuhumar Dan Shugaba Robert Magabe Da Kisan Kai Afrika
Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu Afrika
  • Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo Afrika
  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna Najeriya
  • Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika
  • Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
  • Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
  • Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.