Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana
Published: March 3, 2026 at 3:53 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ayayin da hankalin duniya ya karkata akan yakin da ya barke tsakanin Amurka da isra’ila da Kuma Kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran masana harkokin diplomasiyya na ci gaba da sharhi akan makomar kasashe irin na Africa akan wannan yaki,

Tun bayan kisan jagoran Addini na Kasar ta Iran dama wasu manyan Jami,an Gwamnatin Kasar ciki harda tsohon Shugaban Kasar Ahmadi Najad aka shiga fargaba akan yadda zata kasance da Kuma yadda yakin zai shafi Sauran kasashen duniya,

Tsohon jakadan Najeriya a Kasar Afrika ta Kudu Ambasada Ahmed Musa Ibeto yace ko shakka babu Wannan yaki zai shafi kasashen Afrika Musamman Najeriya ta fuskar tattalin Arziki saboda haka akwai bukatar karatun ta natsu.

Dr. Abubakar kawu Hassan Malami ne a kwalejin ilimi ta Ummaru sanda Ahmadu dake Birnin Minna yace lamarin ba karamin bala’i bane domin kuwa ya shafi Addini kai tsaye.

A yanzu dai lokaci ne yayi da sauran kasahen larabawa dake gabas ta tsakiya suyima kansu karatun ta natsu akan abinda yake faruwa da kasar ta irin da abaya kasar Amurka tayi Amfani da ita wajan tarwatsa kasar Iraqi wannan shine ra’ayin Dr. Ishaka Ibrahim na kwalejin ilimi ta jihar Neja.

Ayanzu dai masanan siyasar duniya na Ganin Koba komi Shugaban Amurka ya Fara cimma maradunsa na biyawa yahudawa Bukata kamar yadda ya dauko alkawari tunda farko kamar yadda Ambasada Ahmed Musa Ibeto ya bayyana.

Ayanzu dai kallo ya Koma gabas ta tsakiya ayayin da ake ci gaba da luguden wuta tsakanin kasar ta Iran da Isra’ela da kuma uwargijiyar Kasar yahudun Wato Amurka.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/YAKIN-IRAN2-3-2026.mp3
Afrika, Amurka, Labarai, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Wasu Mayakan ‘Yan Tawaye Sunkai Hari Filin Jirgin Saman Kasar Kwango
Next Post: Hanyar Gombe Dukku Darazo Ta Zamo Abun Damuwa Ga Al’ummar Arewa Maso Gabashin Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai Afrika
Asusun IMF Zasu Ziyarci Kasar Gabon Afrika
Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Kotun Amurka Tana Tuhumar Wani Dan Jarida Amurka
  • Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
  • An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
  • Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya Ta Bawa Gwamnan Kebbi Mukamin Kyautata Harkar Kiwo Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.