Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Jami’ai A Afirka Sunce Tashin Farashin Mai Kalubale Ne Ga Tattalin Arziki
Published: March 14, 2026 at 7:13 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jami’ai a Afirka suna gargadin cewa tashin goron zabbi da farashin mai yayi sakamakon yakin Iran, zaiyi kalubale ga manufofin tattalin arziki, kuma zaiyi illa ga a wasu muhiman sassa kamar hakar ma’adinai, wadda hakkan zai dagula farfadowar tattalin arzikin kasashe da suke nahiyar.

Manyan bankuna a birane daga Accra zuwa Luanda suna ta rage kudin ruwa a cikin watannin baya bayan nan ganin yadda ake samun faduwar farashin kayayyaki, da kuma samun daidaito a fannin canjin kudaden ketare, da nufin zaburadda tattalin arzikin su. Da alamun yanzu wadannan matakan za su tsaya.

Babban bankin Uganda ne kadai a nahiyar tun ma gabannin fara yakin ya fara taka-tsan-tsan, yanzu yace zai sake nazarin tasirin manufofin ganin sabon kalubalen.

A ranar Alhamis, babban bankin Angola bai rage ko ya kara kudin ruwan da bankuna suke caji a kasar ba, har aka ji gwamnan babban bankin Manuel Tiago Dias yana cewa, kasadar da tattalin arzikin Kasashen ke fuskanta shine tsawon lokaci da yakin zai dauka, wadda zai shafi jigilar taki da sauran su.

Haka nan ana sa ran cewa wasu manyan bankunan kasashe da suke yankin kama daga Ghana, da Najeriya, da Zambia, da ma Kenya duk za su dakatar da matakan sassauta kudin ruwa da bankunan suke karba.

Afrika, Labarai, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata
Next Post: MDD: Fiye Da Farar Hula Metan 200 Suka Mutu A Sudan

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
Farashin Danyen Mai A Amurka Ya Tashi Afrika
Majalisar Dokokin Kamaru Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye Afrika
Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai
Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa Labarai
  • Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
  • An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
  • An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Yayi Magana Game Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Najeriya
  • Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka
  • Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa Amurka
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.