Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran
Published: March 17, 2026 at 4:16 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasashen da suke yankin Gulf da farko ba su goyi bayan Amurka ta kai hari kan Iran ba, amma yanzu suna kira da Amurka kada ta dakatar da yakin, ta yadda zata kyale gwamnatin da take Tehran da zata ci gaba da barazana ga kadarorin mai da tattalin arzikin da suka dogara akan su, kamar yadda kamfanin dilancin labarai na Reuters yaji daga majiyoyi uku a yankin na Gulf.

A lokaci daya kuma,wadannan majiyoyi da kuma jakadun kasashen larabawa da suke aiki a kasashen yammacin duniya 5, sunce Washington tana matsawa kasashe da suke yankin Gulf da su shiga yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran. Kamar yadda uku daga cikin su suka fada, shugaba Trump yana so ya nuna cewa kasashe dake yankin suna goyon bayan yakin, domin hakan zai nuna cewa duniya tana goyon bayan matakin, hakan kuma zai karawa yakin goyo bayan Amurka.

“Akwai tunani a duk fadin yankin Gulf cewa, Iran ta wuce gona da iri kan duk wata kasa dake yankin,” inji Abdulaziz Sager, shugaban wata cibiya mai nazari a Saudiyya, wanda yana sane da irin tunanin gwamnati kan wannan rikici.

“Da farko mun kare su, muka ki goyon bayan yakin,” inji Abdulaziz, “amma da zarar suka fara auna hare haren su akan mu, sun zama makiya. Kuma babu wata hanyar da za’a kalle su.

Ahalinda ake ciki kuma shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana fushinsa kan kasashe da suke yammacin duniya wadanda kawayenta ne, saboda sunyi biris da kiran da yayi na cewa su tura jiragen yaki na ruwa domin su taimaka wajen bude mashigin ruwan Hormuz. Yace Amurka ta tallafa ta kuma kare su, amma ga yanzu yadda suke saka mata. Kasashen Jamus da Japan, da Spain, da Italiya suka ce ba za su tura jiragen su domin tallafawa yakin ahalin yanzu ba.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba
Next Post: An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumomin Kasar China Suna Goyon Bayan Somaliya Labarai
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya Afrika
Kasar Afirka Ta Kudu Ta Tsare Wasu Amurkawa Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • An Kashe Mutane 7 A Unguwar Dorayi Dake Kano Najeriya
  • An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
  • Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar Amurka
  • Sojojin Da Suka Kifar Da Farar Hula A Guinea-Bissau Sun Sanar Da Cewa! Afrika
  • Shugaban Kasar Faransa Ya Zanta Da Shugaban Kasar Iran Afrika
  • Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
  • Barau Jibril: Mu Ba ‘Yan Amshin Shata Bane A Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.