Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
  • Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya Afrika
  • Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai Afrika
  • Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Bukaci Musulmi Su Rungumi Tausayi Da Ƙaunar Juna Afrika

An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC
Published: March 23, 2026 at 7:28 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Zarge-zargen aikata ba daidai ba na lalata da aka yi wa babban mai gabatar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) na ci gaba da kasancewa ƙarƙashin nazari daga ɓangaren zartarwa na kotun, a cewar wata takardar cikin gida da aka rabawa ma’aikata jiya Lahadi, wadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

Babban mai gabatar da ƙara na ICC, Karim Khan, wanda ke binciken laifukan yaƙi, laifukan cin zarafin bil’adama da kuma kisan kare dangi, ya janye daga aikinsa na ɗan lokaci domin ba da dama ga bincike kan zargin cewa yana da wata alaƙar ta cin zarafin wata lauya a ofishinsa ba tare da amincewarta ba. Ya musanta aikata wani laifi.

Lauyoyin Khan sun bayyana a martanin su da suka bayar bayan Reuters ta wallafa rahotonta ranar Lahadi cewa ana sa ran hukumar tafiyar da ICC za ta gana a yau Litinin domin duba shawarwari da sakamakon da wani kwamiti na alkalai masu zaman kansu ya bayar, wanda har yanzu ba a bayyana shi ga jama’a ba.

“Alkalan sun gabatar da cikakken nazari mai zurfi tare da hujjoji, inda suka cimma matsaya gaba ɗaya cewa bayanan gaskiya da aka tattara ba su tabbatar da aikata ba daidai ba ko karya doka ba. Abin da ya rage yanzu shi ne shugabannin siyasa a cikin Hukumar gudanarwa su tabbatar da wannan kimantawa da Kwamitin ya yi,” in ji lauyoyin Khan a cikin wata sanarwar imel.

Afrika, Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf
Next Post: Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci Afrika
Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari Labarai
Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi
  • Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya
  • Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai
  • Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Bukaci Musulmi Su Rungumi Tausayi Da Ƙaunar Juna

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran Amurka
  • An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya Afrika
  • Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin Afrika
  • Rundunar Tsaro Suna Cigaba Da Nasara Akan ‘Yan Ta’adda Tsaro
  • Kasar Amurka Ta Sayi Kamfanin Sada Zumunci Na Tik-Tok Amurka
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.