Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Amurka Da Iran Sun Cimma Yarjejeniya Tsagaita Wuta Na Makonni
Published: April 8, 2026 at 7:05 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya yarda da shirin tsagaita wuta na tsawon makonni biyu da kasar Iran, ana saura sa’o’i biyu kafin wa’adin da ya ba hukumomin Tehran na su bude mashigin ruwan Hormuz, ko kuma ya sa sojojinsa su kai munanan hare-hare a kan cibiyoyi da kayayyakin bukatu na fararen hular kasar domin aiwatar da abinda ya kira shafe jinsin Farisawa daga doron kasa.

A nata bangaren, Iran ta ce za a fara tattaunawa tsakaninta da Amurka ranar jumma’a a Islamabad, babban birnin Pakistan, kasar da firayim ministanta ya shiga tsakani domin ganin an cimma tsagaita wutar.

Har ya zuwa wannan lokaci, Amurka ba ta tabbatar da yin tattaunawa ido da ido tsakanin kasashen biyu ba, amma ta ce ana tattauna hakan.

Shugaba Trump yace Iran ta gabatar da wasu ka’idoji guda 10 wadanda yace ana iya amfani da su a zaman harsashin yin shawarwari, kuma yana sa ran za a kammala a rattaba hannu a kan yarjejeiya cikin wannan wa’adi na makonni biyu.

Trump yace wannan tsagaita wuta da aka cimma daiai lokacin da aski ke zuwa gaban goshi a wa’ad9n barazanarsa, ta dogara a kan cewa Iran zata kyale a c gaba da jigilar mai ta mashigin ruwan Hormuz.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya fada cikin wata sanarwar da ya bayar cewa Iran zata dakatar da kai hare-haren ramuwar gayya, kuma zata bari jirage su shige cikin lumana ta mashigin ruwan na Hormuz.

Gidan telebijin na Iran ya ce shugaba Trump ya amince da ka’idojin da Iran ta shimfida na kawo karshen yakin, tana mai bayyana hakan a zaman ba da kai bori ya hau ga shugaban na Amurka.

Kakakin fadar White House Karoline LEavitt ta maida martani da cewa gaskiyar magana ita ce shugaba Trump da karfin sojojin Amurka suka sa Iran ta yarda zata sake bude mashigin ruwan Hormuz, kuma za a ci gaba da tattaunawa.

‘Yan mintoci kadan a bayan da shugaba Trump ya bada sanarwar tsagaita wutar, hannayen jari a Amurka sun cira sama. Farashin man fetur ya subuto kasa, inda a Amurka Farashin gangar danyen mai ya fado da kimanin kashi 17 cikin 100.

Wannan sanarwar tsagaita wuta ta shugaba Trump, sauyin alkibla ce ta mai gaba daya daga abinda ya furta ‘yan sa’o’i kafin nan inda yayi gargadin cewa idan har ba a biya masa bukatunsa ba, to zai shafe jinsin Farisawa daga bangon duniya baki daya cikin daren nan da ya shige.

A halin da ake ciki, jaridar New York Times ta buga rahoton cewa wani jami’in Amurka ya shaida cewa Amurka ta dakatar da duk wani harin sojan da take kaiwa kan kasar Iran bisa sharrudan wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu.

Sai dai kuma a wani bangaren gidan telebijin na Channel 12 na Isra’ila, ya ce sojojin kasar sun kai sabbin hare-hare ta sama kan Iran cikin asubahin larabar nan, a bayan da Trump ya bada sanarwar tsagaita wuta.

Gidan telebijin din yace an kai hare-haren ne a saboda Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami a kan Isra’ila.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga
Next Post: Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
Akwai Yiwuwar Iran Da Amurka Su Cimma Matsayar Dakatar Da Shirin Nukiliya Amurka
Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa Labarai
‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayin Shanu Tsaro
Tsofin Shugabanin Kasa Sun Karbi Bakoncin Hafsan Sojin Najeriya Tsaro
Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo Afrika
  • Shugaban Najeriya Tinubu Ya Amince Na Tura Jakadu Labarai
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
  • Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
  • Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027 Afrika
  • RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur Afrika
  • Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.