Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da ginin sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin megawat daya (1MW) a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), domin kawo karshen matsalar duhu da tsadar makamashi da ke addabar jami’ar.
Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN), Dokta Mustapha Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan yayin taron kaddamar da aikin da aka gudanar a cikin jami’ar.
Dokta Abdullahi ya bayyana cewa wannan aiki ya zo da wata sabuwar fasaha ta musamman wadda ko kura ta yi yawa ko kuma hadari ya rufe rana, na’urorin za su ci gaba da bayar da wuta. Haka kuma, akwai tsarin sanya ido ta kwamfuta ko wayar salula domin sanin yadda wutar ke gudana.
“Wannan ba wai kawai sanya fanoni (panels) ba ne; tsari ne da aka hada shi da inbata (inverters), batura da tirasfoma wadanda ke aiki tare cikin tsari daya,” in ji shi.
Ya kara da cewa an riga an kawo muhimman kayayyaki kamar batura na ‘Lithium’ da fanonin hasken rana zuwa jami’ar, kuma an riga an amince da kudaden aikin, don haka ’yan kwangila za su shiga aiki gadan-gadan.
Wannan sabon aiki na zuwa ne daidai lokacin da ake kokarin farfado da wata tsohuwar tashar hasken rana mai karfin 3.5MW wadda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya kaddamar a shekarar 2019.
Tsohon aikin, wanda aka kashe masa Naira biliyan 5.6, ya daina aiki ne tun a shekarar 2021, lamarin da ya jefa jami’ar cikin duhu da kuma dogaro da injinan dizal masu cin kudi.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Jami’ar BUK, Farfesa Haruna Musa, ya dora alhakin lalacewar tsohon aikin a kan rashin saka kwararrun injiniyoyin jami’ar yayin gudanar da shi. Sai dai ya ba da tabbacin cewa a wannan karon za su sanya ido sosai.
“Za mu tabbatar mun kula da wannan aiki yadda ya kamata. Inda aka zaba don kafa wannan tasha wuri ne da muke fuskantar kalubalen tsaro, don haka zai taimaka mana kwarai,” in ji Farfesa Musa.
Dokta Mustapha Abdullahi ya bayyana cewa wannan megawat daya da aka fara da shi a BUK matakin gwaji ne (pilot phase), inda akwai shirin kara karfin wutar zuwa megawat 4.5 nan gaba.
Sannan ya kara da cewa wannan bangare ne na babban shirin gwamnati na raba megawat 150 na hasken rana a fadin jihohi 36 na Najeriya da kuma birnin tarayya Abuja, domin samar da wuta mai rahusa ga al’umma.
Sama da 40,000 ne za su amfana da wannan haske wanda zai Saukaka binciken kimiyya da kyautata rayuwar dalibai a ajujuwa da dakunan kwanansu.


