Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja
Published: May 3, 2026 at 8:30 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su kiyaye dabi’u na gari wadanda za su fito da martabar Nijeriya fili, sannan su kasance jakadu nagari ga kasarsu yayin gudanar da ibada a kasa mai tsarki.

Shettima ya bayyana maniyyata a matsayin wakilan Nijeriya a idon duniya, inda ya bukace su da su nuna kyakkyawar dabi’a ta hanyar bin dokoki da oda na kasar Saudiyya.

Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da yake kaddamar da jigilar maniyyata ta farko na shekarar 2026 a Filin Jirgin Sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Ya nanata cewa gwamnati ta jajirce wajen tabbatar da tsaro, tsari, da jin dadin dukkan mahajjata.

“Ku jakadun Nijeriya ne. Kuna dauke da hoton kasarmu da mutuncin al’ummarmu. Halayenku su nuna tarbiya, tawali’u, hakuri, da gaskiya,” in ji shi.

An fara jigilar ne da mahajjata kusan 500 daga Jihar Kogi zuwa kasar Saudiyya, yayin da jimillar maniyyata 50,000 ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin na bana daga Nijeriya.

Da yake jawabi a wurin taron, Shettima ya bayyana cewa aikin Hajji wata tabbatacciyar yarjejeniya ce tsakanin gwamnatin Nijeriya da ’yan kasa, inda ya ce ya zama wajibi kan gwamnati ta sauke nauyin kula da su, su kuma maniyyata su kare mutuncin kasar.

Ya kara da cewa: “Aikinmu ne mu tabbatar kowane maniyyaci ya yi wannan tafiya ba tare da wata wahala ko fargaba ba. Nasarar wannan aikin ba ta dogara ne kawai kan yawan jiragen da suka tashi ba, a’a, tana ga jin dadin mahajjatanmu da kuma kauce wa duk wata nakasu da za a iya kauce mata.”

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya bayyana aikin Hajji a matsayin wata dama ta musamman da ke bukatar sadaukarwa ga Allah. Ya bukaci maniyyata da su ci gaba da addu’o’i ga Najeriya, musamman kan zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

Haka zalika, ya nemi a taya Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Shettima da addu’a yayin da suke kokarin gyara kasar nan ta hanyar manufofinsu na “Sabunta Fata” (Renewed Hope).

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Kasa (NAHCON), Ismail Abba Yusuf, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa hukumar tana nan kan bakarta na tabbatar da jin dadin ’yan Nijeriya. Ya bayyana cewa hukumar tana fuskantar garambawul karkashin gwamnatin Shugaba Tinubu don tabbatar da gaskiya da kuma sauya fasalin aikin Hajji a kasar.

Taron ya samu halartar Karamar Ministar Abuja, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, da wakilin Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, wadanda duka suka jaddada kudurin gwamnati na ganin an kwashe mahajjata lafiya an kuma dawo da su lafiya.

Afrika, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa
Next Post: Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
Masar Ta Kayyade Farashin Buradi A Kasar Afrika
NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
Ga Alamu Jakuna Za Su Bace A Doron Kasa Nan Da Shekaru 5 Labarai
APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Afrika
Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna Afrika
  • Kudaden Shigan Kasar Namibia Ya Bunkasa Saboda Tashin Farashin Gwal Labarai
  • China Ta Kori Wakilan Majalisar Dokoki Uku A Kasar Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu Labarai
  • Jagoran Adawar Uganda Bobi Wine Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
  • Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
  • Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya. Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.