Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe
Published: May 15, 2026 at 6:59 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Bada agaji ta jihar Gombe wato SEMA da haɗin guiwar Hukumar Bada agajin Gaggawa ta Najeriya wato NEMA da Hukuma wayar da Kan al’umma ta kasar wato NOA  ne suka Ziyarci Garin Dukku a jihar Gombe dake Najeriya domin fadakar da al’umma wanda taron ya gudana a sakatariyar Karamar Hukumar.

A jawabinsa Darakta a hukumar Bada agajin Gaggawa ta jihar Gombe Malam Ibrahim Nalado, ya bayyana cewa akwai Hasashen Samun ambaliyar Ruwan Sama a Sassan ƙasar ciki harda jihar Gombe da wassu kananan Hukumomin jihar.

Nalado ya Jadda da cewa, yana da kyau hukumomin su fadakar dasauran al’ummar da Sarakunan gargajiya Domin sakon ya je Wajen al’umma.

Itama anata gudunmawa Daraktan Hukumar wayar da Kan al’umma a jihar Gombe, Hajiya Maimuna Abubakar ta bayyana Farin cikinta yadda al’ummar Dukku Suka Karbi wannan Sako kana ta bukaci hadakai Domin tinkarar wannan matsala da Ake Hasashen faruwanta.

Anasu gudunmawa Kabiru Idris Molki na Hukumar Bada agajin Gaggawa ta kasar da Injiniya Dahiru Ajiya na Hukumar Bada agaji ta jiha sun zayyano Matsalolin da ake shiga Sakamakon ambaliyar tare da kawo Hanyoyin Kariya Domin Samun tsira.

Sunce Sakamakon taro a Abuja da wakilen jihohin Kasar nan inda aka bayyana Hasashen da zai’iya faruwa yasa gwamnatin jihar Gombe ta Bada umarnin zagayawa Domin fadakar da al’umma Domin Samun kariya.

Anasa Bangaren Mai Lura da Karamar Hukumar Dukku Wanda yasamu wakilincin  Shugaban Sashin ESD Malam Ibrahim Muhammad ya bayyana godiyarsa Bisa wannan ziyarar fadakarwa Daga Hukumomin.

Mai Lura da Karamar Hukumar ya Jadda Aniyar goyon bayan Karamar Hukumar Dukku Wajen Samun nasarar wannan Gangamin Domin Taimakon al’ummar jihar Gombe, Arewa Maso Gabas Dama Najeriya Baki Daya.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe
Next Post: Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

MDD: Fiye Da Farar Hula Metan 200 Suka Mutu A Sudan Afrika
CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika
Ansamu Maganin Da Yake Rage Kitsen Jijiyoyi A Amurka Amurka
Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
Gurbin Yaya Tongo: INEC Ta Tsayar Da 19 Ga Satumba Don Zaɓen Cike Gurbi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya Afrika
  • Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya Afrika
  • Kasar Morocco Ta Kwashe ‘Yan Kasar Daga Sassan Ambaliyar Ruwa Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • Gwamnatin Janhuriyar Nijar Ta Soke Lasisin Wasu Kamfanonin Dakon Mai Afrika
  • Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko Najeriya
  • An Kai Hari Kan Masu Hakar Ma’adanai A Kasar Mali Tsaro
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.