Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
Published: May 16, 2026 at 7:54 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Daga cikin matakan da hukumomin tsaro ke dauka na dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, dakarun sojin Najeriya tare da hadin gwiwar sojojin Amurka sun kai wani gagarumin samame kan maboyar mayakan kungiyar IS a yankin Tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadin hallaka babban jagoransu da ake nema ruwa a jallo, Abu-Bilal Al-Manuki, wanda aka fi sani da Abu-Mainok.

Rahotanni sun ce an gudanar da harin ne a daren jiya bayan samun bayanan sirri da suka nuna inda jagoran kungiyar da wasu manyan kwamandojinsa suke boye.

Majiyoyi sun bayyana cewa samamen ya kuma yi sanadin kashe wasu daga cikin na hannun damansa tare da lalata sansanonin da ake zargin kungiyar na amfani da su wajen tsara hare-hare a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Arewa maso Gabas.

An ce aikin hadin gwiwar ya gudana cikin kwarewa, inda aka yi amfani da bayanan leken asiri da kuma kayan aiki na zamani wajen kai harin ba tare da bata lokaci ba.

Da yake mayar da martani kan nasarar aikin, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, yana mai cewa hakan na nuna muhimmancin zumuncin kasashen biyu wajen yaki da ta’addanci.

“Ina mika godiyata ta musamman ga Shugaba Donald Trump saboda jagorancinsa da kuma goyon bayan da Amurka ke bai wa Najeriya a wannan fafutuka,” in ji shugaban.

Tinubu ya kuma jinjinawa dakarun da suka gudanar da aikin daga bangarorin biyu saboda bajinta da kwarewar da suka nuna wajen aiwatar da samamen.

“Munanan hare-hare irin wannan su ci gaba da fadawa maboyar ‘yan ta’adda a duk inda suke a fadin kasar nan,” in ji shi.

Masana harkokin tsaro na ganin hallaka Abu-Bilal Al-Manuki na iya zama babbar koma baya ga ayyukan kungiyar IS a yankin Tafkin Chadi, musamman ganin yadda ake alakanta shi da shirya hare-hare da safarar makamai a tsakanin kasashen yankin.

A ‘yan shekarun baya-bayan nan, Najeriya ta kara karfafa hadin gwiwar tsaro da kasashen duniya domin dakile matsalar ta’addanci da ta addabi wasu sassan kasar, musamman Arewa maso Gabas.

Afrika, Amurka, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe
Next Post: Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Shari’ar Abubakar Malami Ta Kaura Zuwa Sabon Alkali Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika
Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika
An Gano Wasu Boma Bomai Da Aka Binne A Jihar Neja Najeriya
An Kama Wani Da Abubuwan Fashewa A Zamfara Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
  • Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya Afrika
  • Hawan Nasarawa A Jihar Kano Afrika
  • ‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Isra’ila Ta Kai Hari Cibiyar Makamashin Nukiliyar Iran Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand Kimiya
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.