Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe
Published: May 16, 2026 at 2:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya halarci zaɓen fidda gwani na ƴan majalisan wakilai na Jam’iyyar APC da aka gudanar a gundumar Jekadafari dake Ƙaramar Hukumar Gombe, inda ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali a faɗin jihar Gombe.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan zaɓen, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana gamsuwa da yadda ƴan jam’iyyar suka fito, da kuma yadda aka gudanar da zaɓen cikin tsari a duk faɗin jihar.

Gwamnan, wanda ya yi matuƙar farin ciki, ya yabawa kwamitin gudanar da zaɓen da dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar saboda tabbatar da ingantaccen tsari, zaman lafiya da sahihanci wanda ya bai wa duk masu sha’awar takara damar taka rawar gaban hantsi.

“Dukkanmu iyali ɗaya ne, kuma babu wanda ya yi nasara, babu wanda ya faɗi. A ganina, dukkansu ‘yan APC ne kuma ina ƙira ga kowa a haɗa kai don samun nasarar jam’iyyarmu a babban zaɓe mai zuwa,” in ji shi.

Ya kuma jaddada buƙatar haɗa kai wajen ci gaba da ayyukan gina jam’iyyar APC a Jihar Gombe.

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Za mu ci gaba da aiki tare don cimma buri da muradun al’ummar jihar Gombe.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma nuna farin ciki da yadda ƴan jam’iyyar suka nuna dottaku da sanin ya kamata, yana mai cewa rungumar ɗabi’un demokraɗiyya cikin lumana alama ce mai kyau ga makomar jihar da jam’iyyar.

“Ina farin ciki da ganin yadda jama’a suka rungumi demokraɗiyya kuma suna aiwatar da ita cikin lumana,” in ji shi.

Shi ma da yake jawabi, wakilin uwar Jam’iyyar APC ta ƙasa kuma shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na jihar Gombe, Alhaji Labiru Musa Ƙafur, ya yabawa jam’iyyar reshen Jihar Gombe a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya saboda ɗaukaka manufofin demokraɗiyya da kuma ƙarfafa demokraɗiyyar cikin gida.

“Mun gamsu sosai da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da kuma yadda aka gudanar da shi cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.

Jami’an INEC da masu sanya ido masu zaman kansu ne suka bibiyi yadda zaben fidda gwanin ya gudana.

Masu neman tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya na Gombe/ Kwami/Funakaye; Hon. Sadam Bello da Alhaji Zakariyya Jidda sun samu wakilcin wakilansu, yayin da jagoran zaɓen na gundumar Alhaji Yahaya Ibrahim Maƙeri bayan ya kammala ƙidayan ƙuri’u ya bayyana Sadam Bello a matsayin wanda ya lashe zaɓen a gundumar Jekadafari.

Haka dai lamarin ya kasance a sauran gundumomi daban-daban a jihar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
Next Post: Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara Afrika
Gwamnan Jihar Adamawa Fintiri Ya Koma APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Taki Da Mai Ga Manoma Labarai
Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Kama Wasu Matasa da Ake Zargin Su Da Sara Suka  Labarai
  • Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai Afrika
  • Hukumomin Tsaron Kenya Sunce ‘Yan Kasar Suna Fafata Yaki Da Dakarun Rasha A Ukraine Afrika
  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Kara Sace Mutane A Jihar Naija! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.