Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya
Published: May 28, 2026 at 2:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC domin tunkarar babban zaben kasa mai zuwa, inda ya bayyana kudirinsa na jagorantar yunkurin farfado da dimokuradiyya, tsaro da tattalin arzikin Najeriya.

Da yake jawabi bayan ayyana shi a matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben shugaban kasa, Atiku ya bayyana godiyarsa ga shugabanni da mambobin ADC bisa amincewar da suka nuna masa.

Ya ce jam’iyyar ADC ta nuna cewa dimokuradiyya na nan daram a Najeriya, duk da abin da ya kira matsin lamba da takurawa jam’iyyun adawa daga gwamnatin APC mai mulki.

Atiku ya ce a cikin ADC ana bai wa mambobi damar bayyana ra’ayoyinsu da fafatawa cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa hakan ya bambanta da yadda ake gudanar da siyasa a yanzu.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya zargi gwamnatin tarayya da haddasa rikice-rikice a jam’iyyun adawa ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati da wasu bangarori na shari’a.

Ya kuma yi Allah wadai da ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, , yana mai cewa ana amfani da tsare-tsare irin haka wajen tsoratar da ‘yan adawa.

Atiku ya ce gwamnatin ADC idan ta hau mulki za ta dauki matakai masu tsauri wajen magance matsalar rashin tsaro ta hanyar karfafa rundunonin tsaro, samar da kayan aiki na zamani, horas da jami’ai da kuma inganta walwalarsu.

A bangaren ilimi kuwa, ya yi alkawarin samar da ilimin firamare da sakandare kyauta tare da bai wa matasa horo kan fasahar zamani, kirkire-kirkire da sana’o’i domin rage zaman banza da rashin aikin yi.

Dangane da tattalin arziki, Atiku ya soki gwamnatin APC kan yadda talauci da wahalar rayuwa suka karu a kasar, yana mai cewa gwamnatin sa za ta mayar da hankali wajen samar da ci gaban tattalin arziki mai anfani ga daukacin ‘yan Najeriya.

Ya kuma yi alkawarin ba bangaren lafiya muhimmanci ta hanyar kara zuba jari a cibiyoyin kiwon lafiya da samar da asibitoci na zamani domin rage tafiye-tafiyen neman magani zuwa kasashen waje.

Atiku ya yi kira ga dukkan mambobin jam’iyyar da sauran ‘yan siyasa masu kishin kasa da su hada kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaben kasa mai zuwa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai
Next Post: Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi

Karin Labarai Masu Alaka

Sarkin Kagarko Ya Rasu Yana Da Shekaru 110 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Ya Zamo Sakataren Jam’iya Mai Mulki Labarai
Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika
Wasu Mayakan ‘Yan Tawaye Sunkai Hari Filin Jirgin Saman Kasar Kwango Labarai
Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
  • Tattalin Arzikin Kasar Botswana Zai Farfado Afrika
  • Pakistan Zata Karbi Tattaunawar Rikicin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
  • Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Gabatar Da Gwajin Makami Mai Linzami Afrika
  • Afirka Ta Kudu Da Kenya Sun Bayyana Yaudarar ‘Yan Kasashe Da Yawa Tare Da Sakasu Yaki Labarai
  • Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai Sauran Duniya
  • An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.