Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya
Published: June 13, 2026 at 6:04 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

An shiga jimami a jihar Gombe bayan rasuwar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gombe, Kwami da Funakaye a Majalisar Wakilan Tarayya, Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu a birnin Abuja bayan fama da rashin lafiya na wani lokaci.

Rasuwar tasa ta haifar da alhini a tsakanin iyalansa, abokan siyasa, magoya baya da daukacin al’ummar jihar Gombe, musamman ma al’ummar mazabar da yake wakilta.

Marigayin ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa a jihar Gombe, inda ya yi fice wajen wakiltar al’ummarsa da kuma kokarin kawo ayyukan ci gaba da tallafa wa mabukata a mazabarsa.

A cikin sakon ta’aziyya da ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen dan siyasa mai tushe a tsakanin al’umma, kuma jajirtaccen mai hidimar jama’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa da jiharsa hidima.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce rasuwar Tongo babban rashi ne ba ga iyalansa da al’ummar mazabarsa kadai ba, har ma ga daukacin Jihar Gombe da Najeriya baki daya.

Ya ce marigayin ya yi fice wajen aiwatar da ayyukan raya mazaba, tallafa wa mabukata da kuma kokarin inganta rayuwar al’ummar da yake wakilta a majalisar dokokin tarayya.

A cewar gwamnan, Yaya Bauchi Tongo ya kasance shugaba mai kusanci da jama’a, wanda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da hidimar kasa ta sa ya samu karbuwa da girmamawa daga mutane da dama.

Gwamnan ya kuma tuna da irin gudummawar da marigayin ya bayar a mukamai daban-daban da ya rike, yana mai cewa za a ci gaba da tunawa da shi saboda tawali’unsa, saukin kai da kuma jajircewarsa wajen bunkasa rayuwar al’ummar mazabarsa.

Ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye, Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, , ‘yan majalisar dokoki ta kasa, abokan siyasa da kuma daukacin al’ummar Jihar Gombe.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi tare da bai wa iyalansa da masoyansa hakurin jure wannan babban rashi.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar
Next Post: Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo

Karin Labarai Masu Alaka

Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
Hamas Ta Kwance Damara Afrika
Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai
Jirgi Marar Matuki Yayi Ajalin A Kallah Mambobin M23 9 Tare Da Kashe Kakakin Rundunar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Kasar Ukraine Yace Rasha Tana Bawa Iran Bayanan Sirri Afrika
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • ‘Yan Kasar Cuba Sunyi Zanga Zanga A Ofishin Jakadancin Amurka Amurka
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
  • Nasarawa United Ta Kai Wasan Kusa da Ƙarshe Na Gasar Gusau/Ahlan 2026 Wasanni
  • Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala Afrika
  • Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano Labarai
  • Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.