Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Amurka Ta Cire Takunkumin Da Ta Kakabawa Shugaban Venezuela
Published: April 2, 2026 at 12:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Amurka ta sanar a ranar Laraba cewa ta cire takunkumi da ta kakaba wa shugabar rikon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodriguez, kamar yadda aka bayyana a shafin Ma’aikatar Kuɗi ta ƙasar. Wannan na zuwa ne kasa da watanni uku bayan sojojin Amurka sun kama tsohon shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, a wani samame da suka kai a babban birnin ƙasar.

Gwamnatin Trump ta yi hulɗa sosai da gwamnatin rikon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Rodriguez, wadda tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasa ce kuma abokiyar hulɗar Maduro. Amurka ta aika sakatarorin makamashi da harkokin cikin gida zuwa Caracas, tare da masu zuba jari, ta kuma kulla yarjejeniya da za ta ba Amurka damar sayen man Venezuela.

Haka kuma ta yaba da sauye-sauyen da aka yi a fannonin mai da ma’adinai domin jawo jarin ƙasashen waje, tare da sassauta wasu takunkumi.

A watan Maris, Washington ta amince da Rodriguez a hukumance a matsayin shugabar Venezuela, wanda hakan ya ba gwamnatin ta damar sake buɗe ofisoshin jakadanci tare da sake karɓar ikon kamfanonin Venezuela da ke ƙasashen waje.

Rodriguez ta yi maraba da wannan mataki, inda ta bayyana a wani sako da ta wallafa a shafin X cewa wannan “wani mataki ne na daidaita da ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashenmu.”

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaban Kasar Iran Yace Kasar Bata Da Kiyayya Tsakaninta Da Amurkawa
Next Post: Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
‘Yan Tada Kayar Baya Sun Tayar Da Bom A Maiduguri Labarai
Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
Ansamu Maganin Da Yake Rage Kitsen Jijiyoyi A Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ranar Talata Amurka Da Isra’ila Sun Cigaban Da Kai Farmaki Iran Afrika
  • Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
  • Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya Afrika
  • Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Rundunar Operation Hadinkai Sunyi Nasara Akan ISWAP Da Boko Haram Najeriya
  • Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.