Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai
Published: June 16, 2026 at 9:40 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya al’ummar Musulmi a Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya, har ma da sauran Musulmi a faɗin duniya, murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Bayan Hijira (AH).

A cikin saƙon taya murna da ya fitar domin bikin sabuwar shekarar Hijira, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana farkon sabuwar shekarar Hijira a matsayin lokaci na sabunta ruhi, yin nazari mai zurfi kan rayuwa da kuma ƙara jajircewa wajen bin koyarwar addini, zaman lafiya, tausayi da yi wa bil’adama hidima.

Gwamnan ya ce sabuwar shekarar Musulunci wata dama ce ga al’ummar Musulmi domin su yi waiwaye kan abubuwan da suka gabata, su ɗauki darussa daga gare su sannan su fuskanci gaba da ƙarin imani, fata da ƙuduri.

Ya ce, “Yayin da muke shiga sabuwar shekarar Hijira, ya kamata mu ƙara rungumar kyawawan ɗabi’u na haƙuri, sadaukarwa, juriya da adalci waɗanda Ma’aiki Mai Tsira Annabi Muhammad (SAW) ya nuna a lokacin Hijira.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci Musulmi da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Muharram da sauran watannin da ke gaba wajen ƙara yawaita addu’o’i domin samun ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Har ila yau, ya yi kira da a yi addu’o’i na musamman domin samun wadataccen ruwan sama da kuma nasarar kakar noma, yana mai bayyana fatan cewa sabuwar shekarar za ta zo da ƙarin ci gaba da damammaki ga al’umma.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin al’umma, girmama juna da haɗin kai tsakanin kabilu da addinai daban-daban a jihar da ƙasa baki ɗaya, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofi da ayyukan raya ƙasa da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a domin inganta walwala da yanayin rayuwarsu.

Ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka, masu tsayawa kan koyarwar addini da kuma jajircewa wajen gina al’umma mai zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

A ƙarshe, Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya sanya sabuwar shekarar Musulunci ta kasance mai cike da zaman lafiya, ci gaba da rahama ga jihar Gombe, Arewacin Najeriya da ƙasar baki ɗaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran
Next Post: Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci

Karin Labarai Masu Alaka

Rasha Ta Gargadi Amurka Da Isra’ila Kan Harin Iran Afrika
Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika
  • Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Kasar Ghana Afrika
  • Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai Afrika
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.