Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed
Published: November 29, 2025 at 9:20 AM | By: Mahmud Kwari | Updated: November 29, 2025

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, mataimakin Peter Obi, dan takarar shugabancin karkashin Jam’iyyar LP, a zaben 2023.

Kafofin labarai na cikin gida a Najeriya, sun ruwaito majiyoyi a hukumar na cewa, hukumar ta DSS na tuhumar Yusuf Datti da kalaman tunzura Jama’ar ta kafofin labarai na kasar, musamman ikirarin sa na cewa, ana cikin rudani game da sha’anin kundin tsarin mulkin kasa.

Majiyoyin sunce “A baya bayan nan, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana a kafar talabijin yana mai zargin banagaren shari’a dana rundunar sojin Najeriya da bari a rantsar da shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima”.

Majiyoyin sunce kalaman na sa nada wata manufa da ka iya haifar da rudani , la’akari da sarkakiya da dumamar yanayin siyasar Najeriya.

Sai dai majiyar hukumar ta DSS, tayi bayanin cewa, sammacin da hukumar ta yiwa Yusuf Datti ya bayyana a gabanta baya nufin muzgunawa, amma tattaunawa dashi akan batutuwan daya bijiro dasu, ka iya bada damar daukar matakan da suka dace, domin kare gurguwar fahimtar haifar da yamutsin da ba’a zato a tsakanin al’uma.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar ta DSS dake karin haske game da sammacin da ta aikawa Yusuf Baba-Ahmed.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika A Wannan Makon
Next Post: Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Koriya Ta Arewa Ya Goyi Bayan Iran Wajen Zaben Sabon Jagora Mojtaba Khameni Afrika
Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Ce Zata Rika Gudanar Da Harkokin Kasar Venezuela Amurka
Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Shiga Yakin Aiki Afrika
Masu Hakar Ma’adanai 37 Sun Mutu A Jihar Filato Bidiyo
Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
  • Farashin Danyen Mai Ya Farfado Fiye Da Kashi Daya Sauran Duniya
  • Rasha Na Cigaba Da Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Ga Ukrain Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero Afrika
  • Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya Na Shafar Harkokin Jinya A Asibitoci Kiwon Lafiya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 15 A Kasar Australiya Labarai
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.