Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Gombe Da UNFPA Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Yaƙi Da Cutar Fistula Da Tamowa
Published: July 5, 2026 at 7:18 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Gombe ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar kula da mata masu fama da cutar yoyon fitsari sakamakon haihuwa (Obstetric Fistula) da kuma cibiyar kula da yara masu matsanancin tamowa a Babban Asibitin Deba, da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba.

Da yake ƙaddamar da cibiyoyin a madadin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamnan jihar Gombe, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya ce aikin ya nuna ƙudirin gwamnati na ci gaba da inganta harkokin kiwon lafiya da kare lafiyar al’umma.

Ya bayyana cewa tun bayan hawan gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya a shekarar 2019, an mayar da harkokin lafiya cikin manyan manufofin ci gaban jihar ta hanyar gina cibiyoyin lafiya masu aiki na sa’o’i 24 a dukkan gundumomi 114 na jihar, faɗaɗa kayayyakin more rayuwa na kiwon lafiya da kuma aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi lafiyar jama’a.

Dakta Jatau ya ce an gina da kuma tanadi cibiyar kula da masu cutar fistula ne da tallafin Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai Kula da Yawan Jama’a (UNFPA), sakamakon haɗin gwiwa da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Jihar Gombe.

A cewarsa, cibiyar za ta samar da cikakkiyar kulawa ga mata masu fama da cutar fistula domin dawo da lafiyarsu, mutuncinsu da kuma martabarsu a cikin al’umma, yayin da cibiyar kula da yara masu matsanancin tamowa za ta taimaka wajen rage mace-macen yara ta hanyar ba su kulawa ta musamman.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya, shugabannin al’umma da mazauna yankin da su tabbatar da kula da cibiyoyin yadda ya kamata domin su ci gaba da anfani ga al’umma. Haka kuma ya buƙaci jama’a su rungumi rigakafi da sauran matakan kariya daga cututtuka domin inganta lafiyar al’umma.

Tun da farko, Babban Sakataren Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Ali Jalo, ya ce ƙaddamar da cibiyoyin wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da kowa ya samu ingantacciyar kulawar lafiya, musamman mata, jarirai da yara.

Shi ma Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar Gombe, Idris Yambiyu Buba, ya yabawa abokan hulɗa na ci gaba bisa gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa harkokin lafiya a jihar, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da su.

A nasa jawabin, wakilin Hukumar UNFPA ya ce cibiyar za ta ƙara ƙarfafa yaƙi da cutar fistula a jihar, yana mai bayyana cewa Yamaltu Deba na daga cikin yankunan da ke da yawan masu fama da cutar. Ya ƙara da cewa mata 151 sun amfana da shirin kula da cutar a shekarar 2025 ta hanyar haɗin gwiwar Gwamnatin jihar Gombe da gwamnatin Norway ta hannun UNFPA.

Shi kuwa wanda ya kafa ƙungiyar Taimaka, Dakta Abubakar Umar, ya bayyana cewa cibiyar kula da yara masu tamowa tana da gadaje 203 tare da shirin faɗaɗa su zuwa 250. Ya ce cibiyar na da likitoci bakwai da ma’aikatan jinya sama da 50, kuma tana ba da magani kyauta ga duk yaran da ke buƙata.

Sarkin Deba, Alhaji QS Ahmed Usman, da Shugaban Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, Alhaji Yunusa Yakubu, sun yabawa gwamnatin jihar da abokan hulɗarta bisa samar da cibiyoyin, tare da kira ga iyaye su guji auren yara ƙanana, wanda suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cutar fistula.

An kammala bikin ƙaddamarwar da gabatar da shaidun wasu mata da suka warke daga cutar fistula, tare da miƙa kayan aikin jinya, magunguna da sauran kayayyakin kula da marasa lafiya ga cibiyoyin.

Afrika, Kimiya, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Rumbun Hotuna, Sana'o'i, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass
Next Post: Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz

Karin Labarai Masu Alaka

Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu Siyasa
Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai
An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique Afrika
  • An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika
  • Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
  • Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara Afrika
  • Kasar Ghana Ta Umarci ‘Yan Kasar Su Daina Zuba Jari A Kasashen Waje Afrika
  • Shugaba Trump Ya Janye Karbar Kudin Fito Daga Wasu Kasashen Turai Amurka
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.