Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Amurka Zata Kara Tura Sojoji Gabas Ta Tsakiya
Published: March 21, 2026 at 7:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar mayakan Amurka zata tura karin dubban sojojin kundubalarta zuwa gabas ta tsakiya, kamar yadda wasu jami’ai suka fadawa kamfanin dillanciin labarai na Reuters jiya jumma’a, yayinda shugaban Amurka Donald Trump ya zargi kawayen Washinghton dake kungiyar tsaro ta NATO da cewa su ragaye ne saboda sun gaza tura dakarun su su taimakawa wajen bude mashigin ruwan Hormuz.

Mashigin ruwan, inda ta nan ne ake bi da kashi 20 cikin dari na mai da iskar gas da duniya take amfani dashi, kusan Iran ta rufe shi baki daya, tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da yaki kan Iran kusan makonni uku da suka wuce.

Kadarorin mai a Iran da kuma kasashe makabtanta duk an kai musu hari, saboda haka farashin mai ya tashi da kusan kashi 50 cikin dari tun bayan fara yakin ranar 28 ga watan Febwairu, wanda hakan yake barazana ga tattalin arzikin duniya.

An kashe mutane fiye da dubu biyu-galibin su a Iran da kuma Lebanon, su kuma Amurkawa da suke fuskantar tsadar mai, suna kara nuna damuwa ganin alamun yakin zai fadada.

Wata kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a da kamfanin dillancin labarai na Reuters da IPSOS suka gudanar, rabin Amurkawa sun hakikance cewa shugaba Trump zai tura sojojin kasa domin yakin, inda kashi 7 cikin dari ne kawai suke goyon bayan matakin haka.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hawan Sallah Daga Masarautar Kaltungo
Next Post: Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani Afrika
Amurka Ta Kama Wani Jirgin Dakon Mai Amurka
EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai
NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027 Afrika
Yau Litinin Za’a Mika Daliban Ga Iyayen Su Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
  • Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
  • Mutane Da Yawa Ke Mutuwa A Dalilin Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba Kiwon Lafiya
  • Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika
  • Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe Labarai
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
  • Afrika Ta Kudu Ta Dora Haraji Mai Yawa Kan Karafa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.