Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa
Published: July 8, 2026 at 4:24 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Zauren Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya ya ƙaddamar da Kwamitin Amintattu na Asusun Tsaron Arewacin Najeriya a wani sabon yunƙuri na ƙarfafa matakan da ake ɗauka wajen magance matsalolin tsaro da suka dabaibaye yankin.

Ana sa ran kwamitin zai jagoranci tattara kuɗaɗe da sauran tallafi, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, tare da tallafa wa tsare-tsaren haɗin gwiwa na yanki domin inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihohi goma sha tara na Arewacin Najeriya.

Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana a jihar Gombe, Aliyu Bala Gerengi ya ruwaito cewa an ƙaddamar da kwamitin ne yayin taron Dandalin Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya da aka gudanar a Sir Kashim Ibrahim House da ke Kaduna.

Kuma kwamitin ya ƙunshi mambobi ashirin da ɗaya daga jihohi goma sha tara na Arewa, inda jihohin Bauchi da Kaduna suka samu wakilai biyu kowacce.

An zaɓi mambobin ne bisa gogewa da ƙwarewarsu, ciki har da tsofaffin manyan hafsoshin soji da na ‘yan sanda, ƙwararrun ma’aikatan gwamnati da gogaggun masu gudanarwa.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, ne aka naɗa a matsayin Shugaban Kwamitin, yayin da tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Janar Luther Martin Agwai mai ritaya, zai kasance Mataimakin Shugaban Kwamitin.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, AIG Sunday Babaji, shi ne ke wakiltar jihar Gombe a cikin kwamitin.

Da yake ƙaddamar da kwamitin, Shugaban Dandalin Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya tuna cewa a tarurrukan da dandalin ya gudanar a ranar 2 ga Disamban 2025 a Kaduna da kuma ranar 30 ga Maris, 2026 a Abuja, gwamnonin sun cimma matsaya cewa tabarbarewar tsaro a Arewacin Najeriya na buƙatar matakin gaggawa, haɗin gwiwa da tsari mai inganci.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce duk da cewa Gwamnatin Tarayya ce ke da alhakin tabbatar da tsaron ƙasa, haɗin kan jihohin Arewa yana da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin tarayya ta hanyar musayar bayanan sirri, haɗin gwiwar yanki da ƙarfafa juriyar al’ummomi.

Ya bayyana cewa an kafa Asusun Tsaron Arewacin Najeriya ne domin tara kuɗaɗe da sauran tallafi, inganta haɗin gwiwar hukumomin tsaro, ƙarfafa musayar bayanan sirri da kuma tallafa wa ayyukan jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnan ya ce ƙaddamar da Kwamitin Amintattu shi ne babban mataki na farko wajen aiwatar da kudirin dandalin na tunkarar matsalar tsaro cikin tsari, haɗin kai, gaskiya da ɗorewa.

Ya buƙaci mambobin kwamitin su yi aiki tare da gwamnonin Arewa, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin dawo da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa a yankin.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Alhaji Yayale Ahmed, ya bayyana cewa matsalolin tsaron Arewacin Najeriya suna da sarkakiya, kuma suna buƙatar mafita mai ɗorewa ta hanyar haɗin kai da jajircewa.

Ya tabbatar wa gwamnonin cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya, riƙon amana da ƙwarewa, tare da yin aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki, ciki har da cibiyoyin gargajiya, domin cimma manufofin Asusun Tsaron.

Alhaji Yayale Ahmed ya kuma roƙi gwamnonin da su bai wa kwamitin cikakken ‘yancin gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba, domin ya samu damar sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro
Next Post: Gombe: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙungiyar Masu Fashi Da Damfara Ta Yanar Gizo

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Saudiya Zatayi Gwajin Noman Dabino A Kano Labarai
Ministan Kudin Najeriya: Bamu Samu Kudaden Da Muke Tsammani A Wannan Shekarar Ba Najeriya
An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
Boko Haram Ta Kai Hari Maiduguri Cikin Dare Afrika
Gwamnatin Jihar Gombe Ta Haramta Sana’ar Bola Jari Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
  • Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
  • Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wasu Wakilai Amurka
  • An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato Afrika
  • Amurka Zata Fara Sayar Da Maganin Hana Kiba Da Jin Yunwa Amurka
  • Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.