Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin
Published: July 10, 2026 at 9:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da sakatariyar wucin gadi ta ƙungiyar a birnin Kaduna, tare da yin kira ga shugabannin Arewa da su ƙara haɗa kai domin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaban da yankin ke fuskanta.

An ƙaddamar da sakatariyar ne a gini mai lamba 26 da ke kan titin Muhammadu Buhari Way, tsohuwar WAFF Road, inda kuma aka miƙa motocin aiki domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan ƙungiyar.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kafa sakatariyar wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa ayyukan ƙungiyar da samar da ingantaccen tsari na daidaita manufofi da shirye-shiryen ci gaban jihohin Arewa 19.

Ya ce lokaci ya yi da shugabannin Arewa za su gina kan kyawawan tubalan da magabatan yankin suka kafa, tare da nuna jajircewa da sadaukarwa wajen magance ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

Gwamnan ya jaddada cewa halin da Arewa ke ciki na buƙatar haɗin kai da ɗaukar matakai cikin gaggawa, yana mai bayyana cewa aiwatar da tsare-tsaren da ƙungiyar ta tsara zai taimaka wajen shawo kan matsalolin yankin.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya sake tabbatar da aniyar gwamnonin Arewa na ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunkarar matsalolin yankin. Ya kuma yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa jagorancinsa wanda ya haifar da kafa sakatariyar ƙungiyar.

Shi ma Babban Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Dakta Ezekiel Gomos, ya ce sabuwar sakatariyar za ta inganta gudanar da ayyuka, daidaita manufofi da shirye-shiryen ƙungiyar, tare da ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar da sauran hukumomin yankin da na ƙasa.

Ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da sauran gwamnonin Arewa bisa goyon bayan da suka bayar, yana mai tabbatar da cewa za a yi amfani da sakatariyar da motocin aikin cikin gaskiya da inganci domin cimma manufofin ƙungiyar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta
Next Post: APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027

Karin Labarai Masu Alaka

Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
Farashin Danyen Mai Ya Farfado Fiye Da Kashi Daya Sauran Duniya
IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
Soyinka Ya soki Yawan Jami’an Tsaron Da Ake Bai Wa Seyi Tinubu Najeriya
Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika
NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
  • Gombe Ta Ƙarfafa Ilimin Almajirai Da Tsangaya Don Rage Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta Afrika
  • Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu Afrika
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Jadda Da Aniyar Rage Radadin Talauci Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.