Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jami’an Tsaro Sun Dakile Safarar Makamai Daga Jos Zuwa Jihar Neja
Published: July 14, 2026 at 6:16 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Daga Zainab Babaji a Jos Najeriya

Dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation ENDURING PEACE’ sun yi nasarar cafke wassu batagari shida da ke safarar makamai da take zargin suna kai wa ‘yan ta’adda ne.

Jami’an dake aiki a kauyen Samaru da ke gundumar Zonkwa a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, sun cimma nasarar ne yayin da suke gudanar da aiki a shingen binciken ababan hawa na Samaru.

Sanarwa daga kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Cinonso Polycarp Oteh yace wadanda aka cafken sun amsa cewa suna kan hayar zuwa jihar Neja ne daga garin Jos na jihar Filato.

Sanarwar tace nasarar chapke mutanen da aka yi da misalin karfe 09:40 na safiyar litinin 13 ga watan yuli 2026, wani bangare ne na ci gaba a yunkurin dakile ayyukan ta’addanci da Operation ENDURING PEACE ke gudanarwa a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin samamen da ya kai ga nasarar cafke mutanen a cikin mota mai launin toka da lambar EDO GUE-722-LV.

Makaman da jami’an suka kwato sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda 3 da kananan bindigogi guda 4 da wata mota kirar Marsandi kuma ana kan gudanar bincike.

Operation ENDURING PEACE ta yabawa jama’a bisa hadin kai da ci gaba da ba ta goyon baya tare da bukatar su da su ci gaba da lura da yankunan su tare da kai rahoton mutanen da suke zargi ga hukumomin tsaro da suka dace.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026
Next Post: Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami Afrika
Hadakar Kungiyoyin Sauyin Yanayi Ta Bukaci ‘Yan Siyasa Su Dauki Matakan Kare Muhalli Afrika
Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Afrika
Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola Afrika
Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
  • Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare Afrika
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
  • Pakistan Zata Karbi Bakwancin Saudiya, Turkiyya Da Masar Afrika
  • Sakamakon Rikicin Gabas Ta Tsakiya Farashin Mai Ya Karu Labarai
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
  • Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.