Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

AIG Kwaimo Ya Kai Ziyarar Aiki Gombe, Ya Buƙaci Ƙara Ƙaimi A Yaƙi Da Ta’addanci
Published: July 18, 2026 at 5:44 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe a Najeriya ta karɓi bakuncin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta 12 (Zone 12), AIG Vungmoh S. M. Kwaimo, a wata ziyarar aiki da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tare da zaburar da jami’an ‘yan sanda su ƙara himma wajen yaƙi da aikata laifuka da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Taron, wanda ya gudana a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe, ya haɗa manyan jami’an ‘yan sanda daga sassa daban-daban na jihar da kuma mambobin Kwamitin Hulɗa Tsakanin ‘Yan Sanda da Al’umma (PPRC).

An gudanar da laccoci da tattaunawa domin ƙara ƙwarewar aiki, inganta ayyukan jami’an tsaro da kuma ƙarfafa matakan tabbatar da tsaro a yankin.

A jawabinsa na maraba, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Ahmed Umar Chuso, ya gode wa AIG Kwaimo bisa ziyarar tare da sake jaddada cikakken biyayya da ƙudirin rundunar na ci gaba da gudanar da aikinta bisa manufofin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

CP Chuso ya bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Gombe, yana mai cewa ci gaba da tattaunawa da jami’ai da ƙarfafa haɗin gwiwa na taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga ƙwarin gwiwa, tabbatar da ladabtarwa da kuma inganta gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora wa rundunar.

A nasa jawabin, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, AIG Vungmoh Kwaimo, ya bayyana gamsuwarsa da yadda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ke gudanar da ayyukanta ƙarƙashin jagorancin CP Ahmed Umar Chuso.

Ya yaba da nasarorin da rundunar ta samu da kuma zaman lafiyar da ake morewa a jihar, tare da ƙarfafa jami’ai da su ci gaba da jajircewa domin dorewar waɗannan nasarori.

AIG Kwaimo ya bayyana cewa ziyarar ta Gombe ta biyo bayan irin wannan rangadin duba ayyukan runduna da ya gudanar a Jihar Bauchi.

Ya ce manufar rangadin ita ce tantance yadda ake gudanar da ayyukan ‘yan sanda a dukkan jihohin da ke ƙarƙashin Zone 12, sauraron ƙalubalen jami’ai da kuma samar da mafita ta hanyar tattaunawa mai ma’ana domin ƙara inganta ayyukan tsaro da ci gaba da aiwatar da manufar rundunar ta rashin sassauci ga masu aikata laifuka da ta’addanci.

Haka kuma, AIG Kwaimo ya yabawa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen inganta jin daɗin jami’an rundunar.

Ya ce sauye-sauyen da IGP ya kawo sun fara haifar da sakamako mai kyau, sannan ya buƙaci jami’an da su rama wannan kulawa ta hanyar nuna cikakken biyayya, jajircewa, ƙwarewa a aiki da kuma yi wa ƙasa hidima ba tare da son kai ba.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ƙungiyar Mata Sunyi Kira Ga Jam’iyar P R P Da Ta Dauki Baheejja A Matsayin Mataimakiyar Gwamnan A Bauchi 2027
Next Post: Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe

Karin Labarai Masu Alaka

Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai
Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
  • Tsananta Hukunci Ga Masu Fyade Kan Takaita Cin Zarafin Yara Labarai
  • Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa Labarai
  • Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
  • Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Hadakar Ta Da Amurka Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda Najeriya
  • Arsenal Ba Ta Cikin Tattaunawa Kan Sayen Osimhen Wasanni
  • Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.