Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Arsenal Ba Ta Cikin Tattaunawa Kan Sayen Osimhen
Published: August 18, 2026 at 6:43 PM | By: Bala Hassan

OSIMHEN YA CI GABA DA ZAMA BURIN AL HILAL

Dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya ci gaba da kasancewa babban burin kulob din Al Hilal na Saudi Arabia, kamar yadda mashahurin mai sharhi kan harkar kwallon kafa na Italiya, Gianluigi Longari, ya bayyana.

Longari ya ce Al Hilal na ci gaba da zawarcin Osimhen, duk da cewa kulob din ya fara tattaunawar sayen wasu ‘yan wasa domin karfafa tawagarsa.

Ya bayyana cewa Al Hilal ta cimma yarjejeniyar kashin kanta da dan wasan Chelsea, Pedro Neto, tare da bude tattaunawar cinikayya da Chelsea.

A cewar Longari, dan wasan Manchester City, Savinho, na cikin manyan zabukan da Al Hilal ke duba idan har ba a samu Osimhen ba, yayin da dan wasan Aston Villa, Ollie Watkins, shi ma ya amince da yiwuwar komawa kulob din na Saudi Arabia.

Ya ce Al Hilal na tattaunawa da Aston Villa kan Watkins, amma Osimhen, wanda ke taka leda a Galatasaray, ya kasance **“babban burinsu”**.

A halin yanzu dai, rahotanni sun ce Arsenal ba ta cikin tattaunawar kai tsaye da Galatasaray kan yiwuwar daukar Osimhen a wannan kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

Saboda haka, komawar dan wasan zuwa Emirates Stadium na ci gaba da kasancewa da matukar wahala kafin rufe kasuwar musayar ‘yan wasa.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya
Next Post: Manchester United Na Dab Da Kammala Daukar Carlos Baleba Daga Brighton

Karin Labarai Masu Alaka

Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya Wasanni
Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
Eberechi Eze Ba Zai Buga Wasannin Da Ingila Za Tayiba Arteta Wasanni
Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni
Galatasaray Ta Yi Watsi Da Tayin €150m Daga Al-Hilal Kan Victor Osimhen Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai
  • Jagoran Adawar Uganda Bobi Wine Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
  • Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
  • Fafaroma Leo Zai Ziyarci Kasashen Afirka Amurka
  • Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman Amurka
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
  • Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.