Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe
Published: July 18, 2026 at 9:53 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mutane uku sun rasa rayukansu sakamakon mamakon ruwan sama mai ƙarfi tare da iska da ta afku a wasu sassan jihar Yobe dake arewa maso Gabashin Najeriya cikin dare, lamarin da ya haddasa mummunar barna ga gidaje da kadarori.

Ruwan saman da iskar sun shafi unguwannin Tsohon Nguru, Filin Idi da sauran yankuna, inda gidaje, shaguna, rumfunan kasuwa da katanga suka rushe ko suka lalace.

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da daruruwan mazauna yankunan da abin ya shafa suka rasa matsugunansu sakamakon barnar da ruwan saman da iskar suka yi.

Wani mazaunin yankin, Bukar Adamu, ya ce iyalan da iftila’in ya shafa sun nemi mafaka a gidajen ‘yan uwa da kuma wasu gine-ginen gwamnati bayan gidajensu sun rushe.

Shi ma wani mazaunin yankin, Mustapha Modu, ya bayyana cewa iska mai ƙarfi ta kwashe rufin gidansa. Ya kuma ce wani ƙaramin yaro mai suna Ilya Alhassan ya rasu bayan ɗaki ya rufta a kansa a unguwar Filin Idi.

Mazauna yankunan sun yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyin agaji da su gaggauta kai musu ɗauki tare da samar da kayan agaji ga iyalan da iftila’in ya shafa.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro, Uncategorized

Post navigation

Previous Post: AIG Kwaimo Ya Kai Ziyarar Aiki Gombe, Ya Buƙaci Ƙara Ƙaimi A Yaƙi Da Ta’addanci
Next Post: Arsenal Tana Ci Gaba Da Kokarin Dauko Morgan Rogers

Karin Labarai Masu Alaka

Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
Shugaban Amurka Yayi Barazanar Kulle Wani Dan Jarida Amurka
Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo Afrika
Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika
Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi Afrika
Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Man Fetur A Najeriya Afrika
  • Yanayin Yunwa Yana Kara Ta’azarra A Somaliya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Kasar Ghana Ta Tono Gold Na Miliyoyin Kudade Kimiya
  • Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
  • Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.