Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe ta sanar da ƙara tsaurara aiwatar da dokokin zirga-zirga da ƙa’idojin kiyaye lafiyar masu amfani da hanyoyi a faɗin jihar, a wani mataki na rage take dokokin hanya da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rundunar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bisa umarnin Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, an bayyana cewa yawaitar take dokokin zirga-zirga na haddasa cunkoson ababen hawa, kawo cikas ga zirga-zirga, jawo haɗurran mota da kuma asarar rayuka da dukiyoyi da za a iya kauce wa.
Sanarwar ta gargaɗi cewa duk wanda aka samu da laifin karya dokokin zirga-zirga, har da jami’an tsaro masu aiki, za a hukunta shi bisa tanadin doka.
Haka kuma, za a ƙwace motocin da aka samu suna karya dokokin zirga-zirga, tare da gurfanar da masu laifin a gaban kotu idan bukatar hakan ta taso.
Rundunar ta kuma umarci dukkan jami’anta da su gudanar da aikin tabbatar da bin doka cikin ƙwarewa, gaskiya da ladabi, tana mai jaddada cewa babu wani jami’in ɗan sanda da aka ware daga bin dokokin zirga-zirga.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya yi kira ga direbobin motoci, masu motocin haya, masu tuka babura masu ƙafa uku, masu babura da sauran masu amfani da hanyoyi da su kiyaye dokokin zirga-zirga, su mutunta alamomin hanya, su guji tuki cikin ganganci, tare da ba jami’an tsaro haɗin kai wajen tabbatar da bin doka.
Ya ce bin dokokin zirga-zirga shi ne ginshiƙin tabbatar da hanyoyi masu aminci, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma rage haɗurran ababen hawa.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe ta kuma sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da kare lafiyar jama’a, tabbatar da doka da oda a kan hanyoyi, da kuma inganta al’adar amfani da hanyoyi cikin tsari da bin doka a faɗin jihar.


