Hukumar Raya Yankin Kogin Benue ta Sama (Upper Benue River Basin Development Authority UBRBDA) ta ƙaddamar da rabon takin zamani da sauran kayan tallafin noma kyauta ga manoma a jihohin Gombe, Yobe da Borno, domin ƙara yawan amfanin gona da inganta rayuwar manoma a yankunan karkara.
Shirin, wanda Babban Daraktan Hukumar, Dr. Mahmud Sunusi Muhammad, ke jagoranta, ana sa ran zai amfanar da kusan manoma 5,000 daga al’ummomi 87 da ke cikin yankunan da hukumar ke kula da su kafin ƙarshen daminar shekarar 2026.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon kayan a garin Bajoga da ke Ƙaramar Hukumar Funakaye a jihar Gombe, Manajan Yankin Hukumar na Ofishin Dadin Kowa, Dr. Abubakar Muhammad Bello (Sarkin Shanun Yamaltu), ya bayyana cewa wannan shi ne kashi na farko na shirin, wanda aka tsara domin tantance manoma na gaskiya da za su ci gajiyar tallafin.
Ya bayyana takin da ake rabawa a matsayin mai inganci kuma mai matuƙar amfani, tare da kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da shi yadda ya kamata domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa harkar noma.
A cewarsa, wannan shiri na daga cikin tallafin noma na Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ake aiwatarwa ta hannun Babban Daraktan Hukumar, Dr. Mahmud Sunusi Muhammad.
Ya ce, “Hukumar na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa manoma tare da tabbatar da cewa kayan aikin noma sun isa ga waɗanda suka fi buƙatarsu domin ƙara samar da abinci da ƙarfafa wadatar abinci a ƙasa.”
Baya ga takin zamani, hukumar ta kuma raba buhunan Bagco domin adana amfanin gona, da kuma tarunan kamun kifi ga masu kamun kifi da ke yankunan da kogin ke bi.
Dr. Bello ya bayyana cewa shirin zai shafi masu amfani da ruwan kogin a yankunan sama da ƙasa a jihohin Gombe, Yobe da Borno, tare da burin kai wa kusan mutane 5,000 tallafin kafin ƙarshen kakar bana.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, ciki har da Malam Danjuma Sani Ashaka, Alhaji Gado Malleri, Adamu Chindo, Abubakar Isah, Alhaji Usman Mai Agogo, Dallatu Kinafa, Alhaji Garba Umar Tabacco da Muhammad Bello Ashaka (Katukan Ashaka), sun yabawa Gwamnatin Tarayya da shugabannin Hukumar bisa wannan tallafi da suka ce ya zo a kan lokaci.
Sun bayyana cewa takin zamani, tarunan kamun kifi da buhunan Bagco da aka ba su za su taimaka wajen rage kuɗin noma da kamun kifi, inganta ayyukansu tare da ƙara yawan samar da abinci a al’ummomin da abin ya shafa.
Har ila yau, sun yi alƙawarin amfani da kayan tallafin yadda ya kamata, tare da nuna fatan cewa wannan shiri zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa noma da haɓaka tattalin arzikin yankin.


