Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
Published: August 6, 2026 at 6:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Raya Yankin Kogin Benue ta Sama (Upper Benue River Basin Development Authority UBRBDA) ta ƙaddamar da rabon takin zamani da sauran kayan tallafin noma kyauta ga manoma a jihohin Gombe, Yobe da Borno, domin ƙara yawan amfanin gona da inganta rayuwar manoma a yankunan karkara.

Shirin, wanda Babban Daraktan Hukumar, Dr. Mahmud Sunusi Muhammad, ke jagoranta, ana sa ran zai amfanar da kusan manoma 5,000 daga al’ummomi 87 da ke cikin yankunan da hukumar ke kula da su kafin ƙarshen daminar shekarar 2026.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon kayan a garin Bajoga da ke Ƙaramar Hukumar Funakaye a jihar Gombe, Manajan Yankin Hukumar na Ofishin Dadin Kowa, Dr. Abubakar Muhammad Bello (Sarkin Shanun Yamaltu), ya bayyana cewa wannan shi ne kashi na farko na shirin, wanda aka tsara domin tantance manoma na gaskiya da za su ci gajiyar tallafin.

Ya bayyana takin da ake rabawa a matsayin mai inganci kuma mai matuƙar amfani, tare da kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da shi yadda ya kamata domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa harkar noma.

A cewarsa, wannan shiri na daga cikin tallafin noma na Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ake aiwatarwa ta hannun Babban Daraktan Hukumar, Dr. Mahmud Sunusi Muhammad.

Ya ce, “Hukumar na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa manoma tare da tabbatar da cewa kayan aikin noma sun isa ga waɗanda suka fi buƙatarsu domin ƙara samar da abinci da ƙarfafa wadatar abinci a ƙasa.”

Baya ga takin zamani, hukumar ta kuma raba buhunan Bagco domin adana amfanin gona, da kuma tarunan kamun kifi ga masu kamun kifi da ke yankunan da kogin ke bi.

Dr. Bello ya bayyana cewa shirin zai shafi masu amfani da ruwan kogin a yankunan sama da ƙasa a jihohin Gombe, Yobe da Borno, tare da burin kai wa kusan mutane 5,000 tallafin kafin ƙarshen kakar bana.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, ciki har da Malam Danjuma Sani Ashaka, Alhaji Gado Malleri, Adamu Chindo, Abubakar Isah, Alhaji Usman Mai Agogo, Dallatu Kinafa, Alhaji Garba Umar Tabacco da Muhammad Bello Ashaka (Katukan Ashaka), sun yabawa Gwamnatin Tarayya da shugabannin Hukumar bisa wannan tallafi da suka ce ya zo a kan lokaci.

Sun bayyana cewa takin zamani, tarunan kamun kifi da buhunan Bagco da aka ba su za su taimaka wajen rage kuɗin noma da kamun kifi, inganta ayyukansu tare da ƙara yawan samar da abinci a al’ummomin da abin ya shafa.

Har ila yau, sun yi alƙawarin amfani da kayan tallafin yadda ya kamata, tare da nuna fatan cewa wannan shiri zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa noma da haɓaka tattalin arzikin yankin.

Amurka, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
Next Post: NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Taron Masu Mu’amala Da Kafar Facebook A Kano Afrika
Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi Amurka
  • Motsepe, Daga 2028 AFCON Zata Sauya Daga Shekaru Biyu Zuwa Hudu Wasanni
  • Na Duke Tsohon Ciniki Shirye-Shirye
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
  • Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
  • Gaza Ga Albarusai Ga Yunwa Tsaro
  • Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.