Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro Afrika
  • Atiku: Zaben 2027 Zai Zamo Karo Na Karshe Da Zan Nemi Shugabancin Najeriya Afrika
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika

Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo
Published: August 27, 2026 at 5:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugabannin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a Shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun yi kira ga mambobin kungiyar da su kasance masu bin doka da oda, tare da tabbatar da zaman lafiya da sauran al’umma.

Shugabannin sun yi wannan kiran ne yayin wani taro da suka gudanar a jihar Gombe, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi harkokin kiwo, tsaro, zaman lafiya da kuma ci gaban makiyaya a yankin.

Da yake maraba da tawagar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na jihar Gombe, Alhaji Ardo Chindo Abubakar, ya bayyana jin dadinsa da yadda aka zabi jihar Gombe a matsayin wurin gudanar da taron.

Alhaji Ardo Chindo ya kuma yaba da irin kokarin da gwamnatin jihar Gombe ke yi wajen inganta harkokin kiwo da kuma samar da yanayi mai kyau ga makiyaya.

Ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai duba hanyoyin bude hanyoyin shanu, wuraren kiwo da kuma samar da rijiyoyin ruwa domin rage matsalolin da ke tsakanin makiyaya da manoma.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar na kokarin samar da kasuwar shanu ta kasa da kasa a Gombe, wanda ya ce hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwancin dabbobi da habaka tattalin arzikin jihar.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Nasiru Liman Jalbu, ya gode wa shugabannin jihar Gombe da sauran al’ummar jihar bisa irin kyakkyawar tarbar da aka yi wa tawagar.

Haka kuma, shugaban kungiyar na jihar Borno, Alhaji Musa Maina Harande, ya yaba da yadda aka shirya taron, yana mai cewa tattaunawa tsakanin shugabannin makiyaya na da muhimmanci wajen warware matsalolin da ke addabar harkokin kiwo da zaman lafiya.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka tattauna a yayin taron shi ne batun shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo, wanda shugabannin suka ce ya shafe sama da watanni uku a tsare.

Shugabannin kungiyar sun yi kira ga gwamnonin jihohi da sarakunan gargajiya da su shiga tsakani wajen ganin an saukaka masa tare da samar da hanyar da za a tabbatar da an sake shi.

Sun bayyana cewa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya taka muhimmiyar rawa wajen kokarin samar da zaman lafiya, tare da cewa ya bayar da gudunmawa wajen tallafawa harkokin siyasa da kuma nasarar jam’iyyar APC da zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bayan kammala taron, tawagar ta kai ziyara ga Kwamishinan Ma’aikatar Raya Dabbobi ta Jihar Gombe, Alhaji Salihu Baba Alkali, a ofishinsa.

Da yake jawabi ga tawagar, Kwamishinan ya yaba da irin gudunmawar da kungiyar ke bayarwa wajen bunkasa harkar kiwo da kuma habaka tattalin arzikin kasa.

Alhaji Salihu Baba Alkali Katukan Nafada ya kuma tabbatar wa shugabannin kungiyar cewa zai sake jaddada kiran da suka yi na neman a saki shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo.

Taron ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da oda, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin makiyaya, manoma da sauran al’ummomin yankin Arewa maso Gabas.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Mbappé Ya Yi Hat-Trick Yayin Da Real Madrid Ta Lallasa Real Sociedad 4 Da 1
Next Post: Atiku: Zaben 2027 Zai Zamo Karo Na Karshe Da Zan Nemi Shugabancin Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
Yanbindiga sun Kashe kimanin mutane 30 a yankin kayama ta Jihar kwaran Najeriya Najeriya
Hukumar Raya Birane Ta Rushe Gine-Ginen Da Suka Keta Dokokin Tsara Birane A Gombe Labarai
Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja Labarai
Mabiya Dariqar Tijjaniyya Sunfara Gudanar Da Addu’oi Saboda Tsare Sheikh Sani Khalifa Zariya Afrika
Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fiorentina Ta Yi Tayin Farko Ga Manchester United Kan Zirkzee
  • Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro
  • Za a Fara Kakar Gasar Firimiya Ta Najeriya, NPFL, 2026/27 Yau Juma’a, 28 Ga Watan Agusta
  • Atiku: Zaben 2027 Zai Zamo Karo Na Karshe Da Zan Nemi Shugabancin Najeriya
  • Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rundunar Sojin Amurka Sunfara Ficewa Daga Kasar Sham Amurka
  • Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
  • Kwankwaso: Gwamnatin Kano Tamuce Baki Daya, Tafiya APC Allah Ya Raka Taki Gona! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
  • Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya Labarai
  • Jihar Ekiti Ta Aiwatar Da Dokar Haraji Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.