Cibiyar Sasanta Rikice-rikicen Addinai (IMC) Kaduna, tare da haɗin gwiwar Network of Peace Journalism, Rigar Yanchi, Community Peace Observers (CPOs), Kaduna Peace Justice Forum, da Conflict Mitigation and Management Regional Council (CMMRC), ta bayyana matuƙar damuwarta kan musayar kalamai, sharhin kafafen yaɗa labarai da kuma muhawarar jama’a da suka biyo bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da kuma tsoffin korafe-korafe da suka shafi gwamnatin tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ƙungiyoyin sun ce, duk da cewa muhawara mai ƙarfi ta dimokuraɗiyya, ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma bayyana ra’ayoyi kan tarihi da harkokin mulki muhimman ginshiƙai ne na dimokuraɗiyya mai tasowa, ya kamata a yi taka-tsantsan domin muhawarar siyasa tsakanin manyan jami’an gwamnati na iya sake tayar da rarrabuwar kawuna ta ƙabilanci, addini da bangaranci a cikin al’ummar da har yanzu ke da rauni wajen zaman lafiya.
Sun ce jihar Kaduna ta biya babban farashi sakamakon rarrabuwar kawuna da aka samu a baya, don haka ya kamata a karkata dukkan ƙoƙari wajen warkar da raunukan baya, sulhu da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
A saboda haka, ƙungiyoyin sun yi kira cikin gaggawa ga al’ummar jihar Kaduna, Arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya da su ƙi rarrabuwa tare da fifita mutuntaka da haɗin kai.
Sun buƙaci jama’a daga kowane ƙabila, addini da yanki da kada su bari kalaman siyasa ko rashin jituwar shugabanni su koma sanadin ƙiyayya da rikici a tsakanin al’umma.
Sun ce burin da ya haɗa kowa, wanda ya haɗa da zaman lafiya, tsaro da bunƙasar tattalin arziki, ya fi duk wani bambancin siyasa ko na kashin kai muhimmanci.
Ƙungiyoyin sun kuma yi kira da a rungumi tattaunawa mai ma’ana, shugabanci na gaskiya da kuma ɗaukar nauyin zama ɗan ƙasa nagari, ta hanyar magance tsoffin korafe-korafe ta hanyoyin da hukumomi suka tanada, da nuna tausayi da fahimtar juna, maimakon amfani da bambance-bambancen al’umma wajen cimma manufofin siyasa.
Sun kuma yi kira ga shugabannin al’umma, matasa da shugabannin addinai da su yi taka-tsantsan, tare da jagorantar tattaunawar jama’a zuwa ga fahimtar juna da zaman lafiya.
Ƙungiyoyin sun yaba da matakan da gwamnatin yanzu karkashin Gwamna Uba Sani, da kuma wasu ƙungiyoyi da daidaikun mutane, ke ɗauka domin inganta haɗin kai, cike tsoffin gibin da ke tsakanin al’umma da kuma dawo da amincewar jama’a ga harkokin gwamnati.
Sun ƙarfafa dukkan masu ruwa da tsaki da su ƙara mara wa hanyoyin samar da zaman lafiya a matakin al’umma, tsarin Gargaɗin Farko da Amsa da Wuri (EWER), da shirye-shiryen haɗin kan mabiya addinai baya, domin ƙarfafa zaman tare da haɗin kan al’umma.
A wani kira da suka yi ga shugabannin ƙasa da jihohi, ƙungiyoyin sun tunatar da ’yan siyasa, shugabannin addinai, dattawan ƙasa da sauran fitattun mutane cewa kalaman shugabanni na da matuƙar tasiri a cikin al’ummar da ta ƙunshi ƙabilu da addinai daban-daban, musamman a Kaduna da Najeriya baki ɗaya.
Sun bukaci shugabanni a dukkan matakai da su zama abin koyi wajen haɗa kan jama’a, su rage kalaman da ka iya haifar da tashin hankali, tare da mai da hankali kan haɗin gwiwa wajen gina ƙasa.
Sun jaddada cewa Jihar Kaduna gida ce ga dukkan al’ummominta na asali, daga Arewa zuwa Kudu, Gabas zuwa Yamma.
Sun ce ƙarfin Kaduna a koyaushe yana cikin bambancin al’ummarta, juriyarta da kuma ƙarfinta na zaman tare a matsayin al’umma ɗaya.
“Ba za mu bari rikice-rikicen siyasar jiya su raba mu ba. Tare za mu ci gaba da gina Kaduna mai zaman lafiya, wadata da haɗin kai, da kuma Najeriya mafi ƙarfi,” in ji ƙungiyoyin.


