Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
Published: September 14, 2026 at 11:21 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, NNGF, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira da a kara hadin gwiwa tsakanin gwamnati, masana ilimi da malaman addinin Musulunci mata, domin samar da hanyoyin magance manyan kalubalen da ke addabar Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin wasu taruka daban-daban da ya gudanar da manyan malaman jami’o’i da kuma Ulaman mata daga sassan Arewacin Najeriya a Abuja.

Taron da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Sauran Batutuwa, Honarabul Ibrahim Kabir Masari, ya shirya, ya gudana ne karkashin taken “Consolidating the Renewed Hope Agenda: President Bola Ahmed Tinubu’s Achievements and the Road to 2027.”

Taron ya hada daruruwan masana ilimi da Ulaman mata, domin tattauna matsalolin tsaro, yawan yara da ba sa zuwa makaranta, samar da abinci, ilimin sana’o’i, zaman lafiya da kuma rikicin manoma da makiyaya.

Gwamna Inuwa, wanda kuma shi ne Sakataren Renewed Hope Ambassadors, ya ce Arewacin Najeriya ba zai iya shawo kan kalubalen da yake fuskanta ba tare da amfani da ilimi, kwarewa da binciken masana ba.

Ya bukaci masana da su yi amfani da iliminsu da bincikensu wajen samar da dabarun magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da kara mai da hankali kan ilimin sana’o’i domin bai wa matasa dabarun dogaro da kai.

Dangane da rikicin manoma da makiyaya, Gwamnan ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna, yana mai cewa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta musamman da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata muhimmiyar manufa ce da za ta iya taimakawa wajen sauya fasalin bangaren kiwo da magance rikicin manoma da makiyaya.

Gwamna Inuwa ya kuma yaba wa Ulaman mata kan gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta tarbiyyar iyali, zaman lafiya da hadin kan al’umma.

Ya ce mata malaman addinin Musulunci na da muhimmiyar rawa wajen karfafa zaman lafiya, tarbiyyar yara, kyawawan dabi’u da zaman tare a tsakanin al’umma.

Gwamnan ya tabbatar wa mahalarta tarukan cewa irin wannan tuntuba za ta ci gaba, tare da fadada ta zuwa sauran jihohin Arewacin Najeriya domin karfafa fahimtar juna da samar da hanyoyin aiwatar da manufofin gwamnati yadda ya kamata.

A nasa jawabin, mai shirya tarukan kuma Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Sauran Batutuwa, Honarabul Ibrahim Kabir Masari, ya ce an shirya tarukan ne domin samar da ingantacciyar hanya da gwamnati za ta rika tuntubar masana da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin kasa.

Ya ce tuntubar masana ba wai don siyasa kadai ba ne, illa dai domin amfani da ilimi, kwarewa da bincike wajen nemo mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

A karshen tarukan biyu, mahalarta sun gabatar da takardun matsaya, wadanda suka kunshi shawarwari da kudurorin da aka cimma.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugabannin Kasashen Sahel Sunyi Taro a Mali Afrika
Prime Ministan Pakistan Yace Zai Karbi Bakoncin Tattaunawar Amurka Da Iran Afrika
Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika
Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai
  • Kasar Namibiya Tayi Watsi Da Yarjejeniya Tsakanin Ta Da Kamfanin Total Labarai
  • Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
  • Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka
  • Asusun IMF Ya Bukaci Afirka Ta Kudu Ta Rage Bashin Da Suke Karba Afrika
  • Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri Afrika
  • Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga Afrika
  • Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.