Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Najeriya @ 66: Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Kara Zuba Jari A Noma, Masana’antu Da Bunƙasa Matasa
Published: October 1, 2026 at 7:42 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce kasar ta tsallake wani muhimmin mataki na gyare-gyaren tattalin arziki, inda yanzu gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da wadata da kuma inganta rayuwar ‘yan kasa.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na musamman ga ‘yan Najeriya domin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai, wanda ya gabatar a ranar 1 ga Oktoba, 2026.

Shugaban kasar ya ce shekaru 66 da suka gabata, Najeriya ta fara tafiyar mulkin kanta a matsayin kasa mai ‘yanci, kuma tun daga lokacin kasar ta fuskanci kalubale da dama, ciki har da yakin basasa, mulkin soja, matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da rikice-rikicen siyasa.

Ya ce duk da wadannan kalubale, Najeriya ta ci gaba da tsayawa da kafafunta sakamakon jajircewar al’ummarta.

Tinubu ya bayyana manoma, ‘yan kasuwa, malamai, matasa ‘yan kasuwa da jami’an tsaro a matsayin wasu daga cikin mutanen da ke taimakawa wajen dorewar kasar.

Ya ce burin wadanda suka yi fafutukar neman ‘yancin Najeriya bai tsaya ga samun tuta, taken kasa ko matsayi a tsakanin kasashen duniya ba, illa samar da kasa da za ta bai wa ‘yan kasar damar tsara makomarsu, samun mutunci da ingantacciyar rayuwa.

Tinubu ya kare manufofin gyaran tattalin arziki

Shugaban kasar ya ce kafin shekarar 2023, tattalin arzikin Najeriya na fuskantar matsaloli masu tsanani, inda talauci ke karuwa, abin da ya ce ya tilasta gwamnatinsa daukar matakan gyara.

Ya kwatanta halin tattalin arzikin kasar da mara lafiyar da aka gano yana fama da cutar daji, inda ya ce maganin na iya kasancewa mai wahala da radadi, amma yana da manufar ceto rayuwar mara lafiyar.

A cewarsa, gwamnatin da ta hau mulki ta zabi aiwatar da gyare-gyare maimakon ci gaba da daukar matakan da ke rage radadin matsalar na wani dan lokaci kawai.

Ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar ba su haifar da raunin tattalin arzikin ba, sai dai sun tunkari matsalolin da suka dade suna addabar kasar.

Gwamnati ta ce tattalin arziki na farfadowa

Tinubu ya ce bayan kimanin shekaru uku da rabi na aiwatar da gyare-gyaren, tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaban da ya wuce kashi hudu cikin dari a shekarar 2026.

Ya ce bangaren mai da wanda ba na mai ba sun taimaka wajen wannan ci gaba, yayin da satar danyen mai ta ragu.

Shugaban ya kuma ce hauhawar farashin kayayyaki ta ragu daga matakin da ta kai a baya, an sake gina kudaden ajiyar waje, sannan kasuwar canjin kudaden waje ta samu daidaito.

Ya kara da cewa a shekarar 2025, Najeriya ta samu kudaden shiga mafi yawa a tarihinta daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba, wanda ya haura dala biliyan shida.

Tinubu ya ce wadannan matakai sun taimaka wajen kara karfin tattalin arzikin Najeriya da juriyarsa wajen fuskantar kalubale.

Tinubu: Yanzu za a mayar da hankali kan wadata

Shugaban kasar ya ce bayan shekaru uku na gyara tattalin arziki, abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne samar da wadata da za ta shafi kowa.

Ya ce manufar ba wai kawai kara girman tattalin arziki ko inganta alkaluma ba ce, sai dai samar da yanayin da zai bai wa manoma damar yin noma cikin aminci, masana’antu su samu wutar lantarki mai dorewa, ‘yan kasuwa su samu damar samun bashi, sannan matasa su samu ayyukan yi.

Ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen rage tsadar rayuwa ta hanyar rage kudin samar da kayayyaki da kuma safarar su daga inda ake samar da su zuwa kasuwanni.

Noma da ababen more rayuwa

Tinubu ya ce gwamnati za ta kara zuba jari wajen noman ban ruwa da noman rani, samar da iri da takin zamani, habaka aikin noma na zamani da kuma inganta hanyoyin adana amfanin gona.

Ya ce gwamnati na kuma gina tare da kammala hanyoyi, layin dogo da tashoshin jiragen ruwa domin hada gonaki da masana’antu da kasuwanni.

A cewarsa, idan manomi ya rage kudin samar da amfanin gona, asarar amfanin gona ta ragu, masana’antu suka samu wutar lantarki mai sauki, sannan sufuri ya inganta, hakan zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki a kasuwanni.

Samar da ayyukan yi ga matasa

Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya za ta sanya samar da ayyukan yi, bunkasa sana’o’i da masana’antu a sahun gaba na manufofinta.

Ya ce Najeriya kasa ce mai yawan matasa, kuma wajibi ne a mayar da wannan karfin matasa zuwa hanyar samar da arziki da ayyukan yi.

Tinubu ya ce gwamnati za ta yi amfani da iskar gas wajen samar da makamashi ga sabbin masana’antu, ta tallafa wa kamfanonin da ke kokarin farfado da masana’antun kasar, sannan ta fadada hanyoyin sadarwar zamani zuwa al’ummomin da ba su da cikakkiyar damar shiga tattalin arzikin zamani.

Ya ce gwamnati za ta kuma zuba jari wajen horar da matasa da dabarun da masu daukar ma’aikata ke bukata tare da samar wa ‘yan kasuwar Najeriya ababen more rayuwa da kudaden da za su taimaka musu fadada sana’o’insu.

Tallafawa masu karamin karfi

Shugaban Tinubu ya amince cewa miliyoyin ‘yan Najeriya har yanzu suna fuskantar matsalolin samun abinci, kudin makaranta, kudin magani da kuma kudin sufuri.

Ya ce wadannan matsaloli ba su fara ne sakamakon gyare-gyaren tattalin arzikin shekaru uku da suka gabata ba, sai dai sakamakon matsalolin da suka taru cikin shekaru da dama.

Ya ce gwamnati ba za ta iya kawar da dukkan matsalolin da suka taru cikin shekaru da dama cikin shekaru hudu ba, amma za ta iya sauya alkiblar kasar.

Tinubu ya ce gwamnati za ta karfafa tallafin kai tsaye ga gidajen da suka fi fama da talauci tare da inganta National Social Register, domin tabbatar da cewa tallafi ya isa ga wadanda suke bukatarsa.

Ya kuma ce Nigerian Education Loan Fund (NELFUND) na taimakawa wajen bai wa yara daga iyalai masu karamin karfi damar samun ilimin gaba da sakandare.

Haka kuma, ya ce CREDICORP na bai wa ‘yan Najeriya masu aiki damar samun bashi domin sayen ababen more rayuwa kamar motoci, tsarin samar da hasken rana da na’urorin zamani.

Tinubu ya ce gwamnati za ta yaki talauci

Shugaban kasar ya ce shirye-shiryen tallafin zamantakewa ba su ne madadin samar da wadata ba, illa dai hanya ce ta tallafawa al’umma yayin da kasar ke kan hanyar samun ci gaba.

Ya ce manufar gwamnatinsa ita ce kawar da talauci, ba wai kawai inganta yadda ake tafiyar da shi ba.

Ya ce hakan zai bukaci lokaci, da’a da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa tare da samar da miliyoyin ayyukan yi a fadin kasar.

Tinubu ya ce Najeriya yanzu tana fara wannan tafiya daga wani matsayi da ya fi karfi, saboda gwamnati ta ce ta gyara alkiblar tattalin arzikin kasar.

 

“Lokacin wadata ya fara”

Shugaban kasar ya ce: “Lokacin gyare-gyare ya yi aikinsa. Yanzu lokacin wadata ya fara.”»

Ya ce sabon matakin da Najeriya ta shiga shi ne lokacin da alkawarin kasa zai koma abin da ‘yan Najeriya za su ji a rayuwarsu ta yau da kullum.

Tinubu ya ce yana da yakinin cewa miliyoyin talakawan Najeriya, wadanda suka dogara da aiki, jajircewa da azama, su ne ainihin karfin kasar.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin aiki tare wajen gina kasar, yana mai cewa tafiyar da ke gaba na bukatar jajircewa, amma kasar yanzu tana da alkibla bayyananniya da kuma sabon fata.

Shugaban kasar ya ce Najeriya ta “gyara alkiblarta” kuma ta tsallake wani muhimmin mataki na kalubalen tattalin arziki.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su waiwaya baya, sai dai su ci gaba da tafiya tare da imani da kansu da kuma kasar.

Ya ce burin da ke gaban Najeriya shi ne gina kasa mai yalwa da dama, inda za a raba wadata cikin adalci, kowane yaro ya samu damar cimma burinsa ba tare da la’akari da yanayin da aka haife shi ba, sannan dimbin albarkatun Najeriya su bayyana a rayuwar al’ummar kasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala jawabinsa da yi wa ‘yan Najeriya fatan Barka da Ranar Samun ‘Yancin Kai, tare da addu’ar Allah ya albarkaci Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gombe @ 30, Najeriya @ 66: Inuwa Yace Jihar Za Ta Kara Zama Cibiyar Tattalin Arziki A Arewa
Next Post: Mutfwang Ya Yi Wa Fursunoni 130 Afuwa Yayin Bikin ’Yancin Kan Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Kananan Hukumomi Na Kokarin Karbar Kudadensu Daga Jihohi Najeriya
Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama Afrika
Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu Afrika
Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro Afrika
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Isra’ila Ta Kai Hari Cibiyar Makamashin Nukiliyar Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • NNGF Ta Yi Ta’aziyya Ga Musulmi Kan Rasuwar Nafiu Baba-Ahmed Afrika
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci Afrika
  • Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.