Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Yi Gargaɗi Kan Ɗaukar Doka A Hannu Bayan Kama Mutum 17 Afrika

Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara
Published: October 20, 2026 at 4:57 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya reshen jihar Gombe, ta sake jaddada aniyarta ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Kashe Gobara ta jihar Gombe, domin inganta rigakafin gobara, shirin tunkarar aukuwarta da kuma gaggawar kai ɗauki, gabanin lokacin Harmattan na shekarar 2026.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta jihar Gombe, Mista Idi Musa Kwami, tare da tawagarsa, a ziyarar ban-girma da suka kai hedikwatar hukumar ta tarayya da ke Gombe.

Manufar ziyarar ita ce ƙarfafa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin hukumomin biyu, inganta haɗin kai wajen gudanar da ayyuka, tare da samar da dabarun tunkarar ƙarin haɗarin aukuwar gobara da ake samu a lokacin Harmattan.

Da yake karɓar baƙuncin tawagar a madadin Kwanturola na Jiha, DCF Suleiman Mohammed Suleiman, Shugaban Sashen Kula da Ma’aikata (HRM), DSF Isah Mohammed Lamido, ya tabbatar wa tawagar cewa hukumar a shirye take ta haɗa kai da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe da sauran masu ruwa da tsaki, domin samar da jihar Gombe mai cikakken shiri da kariya daga haɗarin gobara.

Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa, musayar bayanai, wayar da kan jama’a da kuma tsara hanyoyin kai ɗauki cikin haɗin kai, domin rage aukuwar gobara da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Jami’in kula da harkokin ma’aikata ya kuma yi amfani da wannan dama wajen gayyatar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe domin ta taka rawar gani a Makon Wayar da Kan Jama’a kan Kariyar Gobara na shekarar 2026, wanda aka tsara gudanarwa daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Nuwamba, 2026.

An tsara wannan gangami ne domin wayar da kan jama’a kan hanyoyin rigakafin gobara da matakan kariya, musamman ganin yadda lokacin Harmattan ke ƙara haɗarin aukuwar gobara.

Wannan haɗin gwiwa ya nuna irin aniyar hukumomin biyu na samar da muhalli mai aminci ta hanyar ɗaukar matakan rigakafin gobara tun da wuri, ilmantar da jama’a da kuma inganta tsarin gudanar da ayyukan gaggawa.

Saboda haka, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, reshen jihar Gombe, ta yi kira ga mazauna jihar, ‘yan kasuwa, cibiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi matakan kariya daga gobara, tare da yin aiki tare wajen hana aukuwar gobara a lokacin Harmattan da ma bayan sa.

Kariya daga gobara nauyin kowa ne.

A kasance cikin shiri, a hana gobara, a kare rayuka da dukiyoyi.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Gombe: NEDC Za Ta Samar Da Motocin Lantarki Domin Rage Tsadar Kuɗin Sufuri
Next Post: Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim

Karin Labarai Masu Alaka

Pantami, Mailantarki Da Garry Za Su Fafata A Sabon Zaɓen Fidda Gwani Na PDP A Gombe Afrika
Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo Labarai
Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
Burkina Faso Ta Fara Kera Motocin Yaƙi Afrika
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa Amurka
  • Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
  • Akwai Shakku Akan Sanin Wacce Kungiyar Kwallon Kaface Zata Lashe Gasar Kofin Afirka Da Akeyi A Morocco Nishadi
  • An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026 Afrika
  • ‘Yan Sanda A Tsibirin Bahamas Sun kama Mijin Wata Ba Amurkiya Amurka
  • INEC Ta Ce Ta Kammala Shirye-Shiryen Zaɓen Cike Gurbi A Gombe Afrika
  • PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
  • Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.