Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya (NEDC), tare da haɗin gwiwar Renewed Hope da kamfanin Attahir Enterprises Nigeria Limited, ta shirya taron wayar da kan masu ruwa da tsaki kan amfani da motocin lantarki, domin inganta sufuri, kare muhalli da bunƙasa tattalin arziki a yankin Arewa Maso Gabas.
Shirin ya ƙunshi samar da NAPEP masu amfani da lantarki guda 10,000, motocin haya 300 da motocin bas 30, domin rage kuɗin sufuri da makamashi, tare da samar da sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga ga al’umma.
An gudanar da taron a Otal ɗin Custodian da ke Gombe, ƙarƙashin taken “Ƙarfafa Arewa Maso Gabas: Rungumar Sufurin Lantarki Domin Muhalli Mai Tsabta, Ingantaccen Sufuri da Wadata.”
A jawabin maraba, Kodinetan Hukumar NEDC na jihar Gombe, Architect Usman Muhammad, ya bayyana kekunan hawa masu amfani da lantarki a matsayin wata muhimmiyar hanya ta sufuri da za ta taimaka wajen rage kuɗin makamashi da kuma kare muhalli.
Ya ce amfani da motocin lantarki ya samu karɓuwa a wasu ƙasashe masu tasowa, yana mai bayyana fatan cewa shirin zai taimaka wajen samar da sufuri mai ɗorewa da bunƙasa yankin Arewa Maso Gabas.
A nasa jawabin, Rufai Lawan Baba Manu ya buƙaci mahalarta taron, musamman masu gyaran babura da kekunan hawa masu ƙafa uku, da su yi amfani da wannan dama wajen koyon sabuwar fasahar gyaran motocin lantarki.

Ya bayyana cewa duniya na ci gaba da sauyawa ta fuskar fasaha, saboda haka akwai buƙatar masu sana’o’i su rungumi sauye-sauyen domin inganta sana’o’insu da kuma ƙara samun kuɗin shiga.
Rufai Lawan Baba Manu ya ƙara da cewa manufar shirin ba wai kawai maye gurbin injinan mai da na lantarki ba ce, illa gina ingantaccen tsarin sufuri mai tsafta, sauƙin amfani da inganci.
Ya kuma bayyana cewa za a samar da wuraren cajin motocin lantarki guda biyu a Jihar Gombe, domin sauƙaƙa wa masu amfani da motocin samun wutar da za su yi amfani da ita.
A nasa ɓangaren, Babban Jami’in Gudanarwa na Attahir Enterprises Nigeria Limited, Bunu Umar Abacha FG, ya ce shirin zai samar da motocin bas, motocin haya da kekunan hawa masu amfani da lantarki ga al’ummar Arewa Maso Gabas.
Ya bayyana cewa manufar shirin ita ce rage wahalhalun sufuri da kuɗin da jama’a ke kashewa wajen zirga-zirga, tare da sauƙaƙa matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.
A nasu jawaban, Hakimin Doma, Alhaji Abdullahi Doma, da Hakimin Jalo, Waziri Sammani Bappah Yerima, sun yaba wa hukumar NEDC bisa ƙoƙarinta na inganta rayuwar al’ummar yankin.
Sarakunan gargajiyar sun buƙaci mahalarta taron da su mai da hankali wajen koyon dabarun da ake koyarwa, tare da tabbatar da cewa sun yaɗa ilimin ga sauran al’umma domin mutane da dama su amfana.
Tun da farko, Injiniya Emmanuel Wapah ya gabatar da lacca kan fasahar motocin lantarki, dorewar amfani da su da kuma dabarun aiki a wuraren gyaran motoci.
Ya yi bayani kan ma’anar motocin lantarki da muhimman sassan da suka ƙunsa, tare da bayyana bambancin da ke tsakaninsu da motocin da ke amfani da man fetur.
Ya jaddada muhimmancin rungumar hanyoyin samar da makamashi mai ɗorewa, yana mai cewa amfani da motocin lantarki na da damar taimakawa wajen kare muhalli, inganta sufuri da bunƙasa tattalin arziki.
Mahalarta taron sun haɗa da wakilan ƙungiyoyin masu gyaran babura da kekunan hawa, Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Mota ta Ƙasa (NURTW), Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Ƙasa (NARTO), sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin sufuri.
Ana sa ran taron zai ƙara wayar da kan jama’a, inganta ƙwarewar masu sana’o’i da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki wajen rungumar tsarin sufuri mai tsafta da ɗorewa a faɗin yankin Arewa Maso Gabas.


