Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7 Afrika
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe Labarai
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya Afrika
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki Afrika
  • Tinubu Ya Shiga Cikin Ka’aba Ya Yi Addu’a Afrika

Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK
Published: November 4, 2026 at 2:32 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon tsarin bada rancen kuɗi ta hanyar amfani da lambar USSD, wanda zai bai wa ƴan ƙasa damar karɓar rancen kuɗin sayen kayayyaki ta wayoyin hannu na yau da kullum ba tare da buƙatar intanet ko wayoyin zamani ba.

Hukumar Bada Lamuni ta Ƙasar (CREDICORP) ce ta ƙaddamar da sabon shirin mai suna SPARK domin faɗaɗa damar samun rance, musamman ga mutanen da ba su taɓa karɓar rance ba ko kuma ba su da tarihin karɓa da biyan bashi a hukumance.

Hukumar ta bayyana *347*333# a matsayin lambar USSD din, sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa tsarin ya fara aiki a faɗin ƙasar baki ɗaya ba.

CREDICORP ta ce ana sa ran tsarin zai samu karɓuwa da kuma fara aiki a wurare da dama kafin ƙarshen shekarar 2026.

Manufar shirin ita ce bai wa masu karɓar rance damar gina tarihin biyan bashi, wanda zai taimaka wajen inganta matsayinsu na samun lamuni da kuma buɗe musu ƙofofin samun wasu hidimomin kuɗi a nan gaba.

Abubuwan da ’yan Najeriya za su iya karɓar rancen na CREDICORP ɗin sun ƙunshi manyan fannoni guda biyar da aka tsara domin taimaka wa ’yan Najeriya samun muhimman kayayyaki, kayan amfanin gida da kuma kadarorin da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Ga fannoni biyar ɗin:

1. Sufuri: Motocin da ke amfani da iskar CNG da motocin lantarki.

2. Kayan fasahar zamani: Kwamfutocin tafi-da-gidanka, wayoyin zamani da na’urorin kwamfutar hannu (Tablets).

3. Hanyoyin samar da makamashi: Janareto da na’urorin hasken rana (Solar panels).

4. Inganta gidaje: Kayan ɗaki, na’urorin amfanin gida da kayan gini.

5. Muhimman abubuwan rayuwa: Kiwon lafiya, tufafi, abinci da abubuwan sha.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: KADCCAM Ta Yi Gargadi Kan Illolin Kona Daji Da Gurɓata Muhalli
Next Post: Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Amurka Zai Sake Gine Gaza Amurka
An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai
Gwamnatin Amurka Da Najeriya Sunyi Hadakar Inganta Asibiticin Kiristoci Amurka
Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK
  • KADCCAM Ta Yi Gargadi Kan Illolin Kona Daji Da Gurɓata Muhalli
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • ANNOUR Ta Raba Kayan Makaranta Na CFA Miliyan 5.5 Ga Yara A Douala Afrika
  • Gombe: An Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Matar Dan Sanda Afrika
  • Ferfesa Pantami Yayi Watsi Da Amincewa Da Jamilu Isiyaku Gwamna Afrika
  • Gombe Ta Zo Ta Biyu Wajen Aiwatar Da Shirin L-PRES Afrika
  • Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
  • Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.