Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita
Published: December 16, 2025 at 4:11 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Buhari har kulle dakinsa ya dinga yi saboda ya yadda da jita-jitar cewa zan kashe shi  Inji Aisha Buhari

Aisha Buhari, matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ta ce mijinta ya fara kulle ɗakinsa bayan jita-jitar da ta bazu a Aso Rock cewa tana shirin kashe shi.

Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce Buhari ya yarda da abin da ake yadawa, lamarin da ya sa ya sauya wasu daga cikin halayensa.

Aisha ta bayyana ƙwarewarta wajen kula da matsalolin lafiyar Buhari a cikin wani littafin tarihin rayuwarsa mai shafuka 600 mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari” (Daga Soja zuwa Jagoran Ƙasa: Tarihin Muhammadu Buhari).

A cikin littafin, Aisha ta ce matsalar lafiyar da Buhari ya fuskanta a shekarar 2017 ba wata cuta ce mai ban mamaki ba ko sakamakon guba, sai dai ta fara ne bayan rushewar tsarin cin abinci da kuma rashin kula da tsarin gina jiki yadda ya kamata.

Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce tun da dadewa ita ke kula da abincin mijinta a wasu lokuta na musamman, tana mai cewa tsarin ya taimaka wa Buhari wajen kiyaye daidaiton lafiyarsa.

“A cewar Aisha Buhari, matsalar lafiyar mijinta a shekarar 2017 ba ta samo asali daga wata cuta mai ban mamaki ko makirci na ɓoye ba amma ta fara ne da lalacewar tsarin rayuwa; abin da ta kira ‘tsarin abincina’ wato tsarin cin abinci da ƙarin gina jiki da ta dade tana kula da su a Kaduna kafin su koma Aso Villa,” in ji littafin.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje
Next Post: Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
Makarantun Allo Zasu Yi Gogayya Da Na Boko Labarai
Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakai Don Farfaɗo Da Maɗaba’ar Gwamnati
  • Boko Haram Sun Dauke Kansiloli A Borno
  • A Kowacce Rana Kasar China Tana Sayan Danyen Mai Ganga Dubu 600 Daga Kasar Venezuela
  • Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
  • Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai
  • Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya. Wasanni
  • Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai
  • Musa: “Da Yaddar Allah Zamu Ga Bayan Ta’addanci A Najeriya” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna Najeriya
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.