Masu tattaunawar sulhu daga Amurka da Iran sun gudanar da tattaunawa mafi muhimmanci a Pakistan domin yunkurin kawo Karshen yakin da suke tafkawa tsakanin su.Wannan itace tattaunawa mafi muhimmanci da aka taba yi tsakanin kasashen biyu tun bayan juyin juya hali na addini a Iran a shekarar 1979.
Ana ci gaba da tattaunawar duk da shugaban Amurka Donald Trump yace sojojin sa sun nutsar da jiragen Iran masu binne bama bamai, kuma suna bude hanyar mashigin ruwa na Hormuz.
Sojin Amurka sun ce biyu daga cikin jiragen yakin su na ruwa sun wuce ta mashigin ruwan, kuma an yi shirye-shirye da za’a cire bama baman da aka saka a wajen. Amma kafar yada labaran gwamnatin Iran ta Nournews tace wannan labari ba gaskiya bane. Tace ba wasu jiragen ruwan Amurka da suka ratsa ta mashigin ruwan.
Jaridar Financial Times ta Birtaniya kuma tace tattaunawar da ake gudanarwa a Pakistan ta cimma cikas saboda mashigin ruwan na Hormuz.
Mashigin ruwan na Hormuz wanda yake a kudancin gabar teku na Iran na daga cikin abubuwa mafi muhimmanci da za’a tattauna a kai a birnin Islamabad babban birnin Pakistan.


