Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman
Published: February 5, 2026 at 7:46 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Amurka da Iran sun yarda zasu tattauna gobe Jumma’a a kasar Oman, a cewar jami’an kasashen biyu, sai dai kuma har yanzu ba su cimma daidaituwa a kan nacewar da Amurka take yi cewa lallai tattaunawar ta hada har da makamai masu linzami na Iran, yayin da ita kuma take cewa shirinta na nukiliya kawai zata tattauna akai.

Wannan yunkurin na diflomasiyya yana zuwa a yayin da Amurka take ta girka sojoji a yankin gabas ta tsakiya, su kuma kasashen yankin suke kokarin ganin an kaucewa fadan soja da suke fargabar cewa zai iya yaduwa zuwa fadin yankin.

Sabanin ra’ayi a game da abubuwan da za a tattauna a kai sun janyo tababa a kan ko za a iya yin zaman, abinda zai haifar da yanayin da shugaba Donald Trump na Amurka zai iya yin amfani da shi don aiwatar da barazanarsa ta kai hari a kan Iran.

Jami’an Amurka da na Iran sun ce sassan biyu sun yarda za a gudanar da wannan taron a Muscat, babban birnin Oman, a bayan da tun farko aka ce za a yi ne a Istanbul na Turkiyya.

Amma babu wata alamar dake nuna cewa sun cimma daidaituwa a kan ajandar wannan taron.

Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Hare Hare Daban Daban A Najeriya
Next Post: Kasar Amurka Da Rasha Zasu Kawo Karshen Tsagaita Nukiliya

Karin Labarai Masu Alaka

Ana Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Trump Da Zelensky Domin Tsagaita Wuta A Ukraine Labarai
Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
Gwamnatin Shugaba Trump Tana Cigaba Da Janye Jakadunta Zuwa Gida Amurka
Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai
‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 15 A Kasar Australiya Labarai
‘Yan Tada Kayar Baya Sun Tayar Da Bom A Maiduguri Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana
  • Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani
  • Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Al’ummomin da Ambaliyar Ruwan Mokwa a Jihar Nejan Najeriya ta sharewa gidaje sun Koka. Najeriya
  • Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
  • Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
  • Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
  • Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.