Jami’an leken asirin Amurka sun dakatar da bawa kasar Isra’ila bayanan leken asiri masu muhimmanci na wani dan lokaci a zamanin gwamnatin shugaba Biden, a saboda damuwa kan yadda Isra’ilar take gudanar da yakin Gaza.
Wasu jami’ai 6 dake da masaniya game da lamarin sun fada ma kamfanin dillancin labarai na AP cewa a cikin shekarar 2024, Amurka ta tsinke nuna ma Isra’ila hotunan bidiyo kai tsaye na wani jirgin drone na Amurka dake shawagi a samaniyar Gaza, bidiyon da Isra’ila tayi amfani da shi wajen farautar mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma ‘yan rajin Hamas.
Majiyoyin suka ce an shafe kwanaki da dama ba a barin Isra’ila ta kalli bidiyon.
Wasu daga cikin wadannan majiyoyi sun ce Amurka ta kuma takaita yadda isra’ila zata iya yin amfani da bayanan leken asirin da Amurka take ba ta wajen farautar cibiyoyin soja.
Wannan shawarar tazo a daidai lokacin da hukumomin leken asirin Amurka suka kara nuna damuwa a kan fararen hular da sojojin Isra’ila suke kashewa a Gaza amma jami’ai sun kuma damu da cewa hukumar tsaron cikin gida ta Isra’ila da ake kira Shin Bet, tana cin zarafin Falasdinawa da ake kamawa a zaman fursunoni.
Jami’an leken asirin na Amurka sun damu cewa Isra’ila ba ta bayar da kwakkwarar tabbacin cewa zata yi aiki da dokokin yaki na kasa da kasa wajen yin amfani da bayanan da ta samu daga Amurka ba.
A karkashin dokokin Amurka, tilas ne hukumomin leken asirin Amurka su samu wannan tabbacin kafin su iya bawa wata kasar waje wani bayani.


