Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Amurka Zata Fara Sayar Da Maganin Hana Kiba Da Jin Yunwa
Published: December 25, 2025 at 8:44 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masu fashin baki sun ce amincewar da aka yi da fara sayar da wani maganin rage kiba da rage jin yunwa wanda za a fara sayarwa a nan Amurka cikin watan Janairu mai zuwa, zai tilasta ma kamfanonin sarrafa abinci da gidajen sayar da abinci baki daya sauya irin abubuwan da zasu iya sayarwa da jama’a.

Da ma akwai wannan magani da ake yin allurarsa, amma wannan shine karon farko da aka amince da sayar da shi a zaman kwayar da mutum zai iya hadiya kuma masana suka ce ana sa ran miliyoyin Amurkawa zasu sayi kwayar maganin maimakon allurar a saboda ya fi araha, kuma zai fi dadin amfani maimakon yi ma kai allura a kullum.

A ranar litinin ne Hukumar Kula da Tsarin Abinci da Magunguna ta Amurka ta amince da wannan magani mai suna WEGOVY GLP-1, abinda ya sa hannayen jari na kamfanonin sarrafa abinci suka fadi kasa warwas a kasuwannin hada-hadar jari.

Da ma allurar wannan maganin da aka fara amfani da ita a can baya ta sa manyan kamfanonin sarrafa abinci irinsu Nestle da gidajen sayar da abinci sun fara ganin yadda kasuwar kayayyakinsu take yin kasa.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Ukraine Tana Cigaba Da Tattaunawa Da Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Kasar
Next Post: Amurka Ta Kai Hari Kan ‘Yan ISISI A Jihar Sakkwato Bisa Rokon Gwamnatin Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela Amurka
Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka
Ana Zargin Cewa ‘Yan Bindiga Biyun Nan Mambobin Kungiyar ISIS Ne Amurka
Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman Amurka
Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka Biyu Amurka
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • An Kashe Mayakan Sakai 67 A Pakistan Sauran Duniya
  • Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni
  • Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi Labarai
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata Labarai
  • Yeriman Ingila Ya Mayarwa Trump Martani Amurka
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar Siyasa
  • Yawan Mai Da Kasashen OPEC Suke Hakawo Yayi Kasa Sosai Labarai
  • Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.