Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani
Published: July 1, 2026 at 9:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar APC ta cire tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, da wasu ‘yan takarar kujerar Sanata biyar daga cikin jerin sunayen ƙarshe da ta miƙa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Haka kuma, jam’iyyar ta cire tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Ondo, Gbenga Elegbeleye, tare da maye gurbin wasu ‘yan takarar majalisar wakilai guda 19 da suka yi nasara a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Mayun 2026.

A cikin wata wasiƙa da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ajibola Basiru, suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta bayyana cewa sauye-sauyen sun biyo bayan rahoton Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen fidda gwani.

Jihohin da sauye-sauyen suka shafa sun haɗa da Abia, Kogi, Taraba, Benue, Ebonyi, Ondo, Kaduna, Neja da Kwara.

Sai dai APC ta tabbatar da sunayen wasu fitattun ‘yan takara da za su fafata kujerun Sanata, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, da gwamnoni AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Hope Uzodimma na Imo, Ahmadu Fintiri na Adamawa da Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe.

Jam’iyyar ta ce ta karɓi sama da ƙorafe-ƙorafe 700 daga mambobinta dangane da zaɓen fidda gwani. Ta ƙara da cewa a halin yanzu fifikonta shi ne tabbatar da cewa duk ‘yan takarar sun cike takardun tsayawa takara tare da loda su a manhajar INEC kafin cikar wa’adin ranar 10 ga Yulin 2026.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas
Next Post: NITDA Da GOSIDEC Sun Horar Da Ma’aikatan Gombe Don Inganta Ayyukan Gwamnati

Karin Labarai Masu Alaka

Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
Tashoshin Mai Basa Iya Loda Mai A Rasha Labarai
Motar Kungiyar Kwallon Kafar Bayelsa United Ta Yi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kasar Saudiya Zatayi Gwajin Noman Dabino A Kano Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark Afrika
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Rahoton MDD Yace An Kashe Fiye Da Farar 1000 A Sudan Labarai
  • Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika
  • JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika
  • Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
  • Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.