Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta gudanar da babban taro na kasa inda ta amince da mukaman dukkanin shugabannin jam’iyyar ba hamayya.

Taron dai wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja , ya samu halartar dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga fadin Najeriya.
“Masu sukar cewa mu na neman maida Najeriya kasa mai bin jam’iyya daya ba haka ba ne, don ni na yi amanna da gasa a tsarin dimokradiyya amma hakan bai haramtawa kowa yin hulda da abokan siyasa ko jam’iyyar da ta kwanta ma sa a rai ba” Inji shugaba Tinubu a jawabin da ya gabatar cikin salon jawabinsa na magana daya bayan daya sannu-sannu kwana nesa.
Shugaban wanda ya nuna akwai kwarin guiwar gyaruwar lamura na kuncin tattalin arziki da a ke fuskanta, ya bukaci a yi shiru na minti daya don karrama marigayi shugaba Buhari da wani minti daya don sauran wadanda su ka kirkiro APC amma kuma sun kwanta dama.
Nan take a ka rantsar da shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin Nantawe Yilwatda daga jihar Filato.
Mataimakin sakataren kudi na jam’iyyar Ambasada Haruna Gimsau ya ce ba sabon abu ba ne daidaitawa wajen fidda shugabannin jam’iyya.
Ita ma mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar Zainab Abubakar wacce ta sauko daga dandalin rantsarwa ta na annashuwa, ta ce hakan kwarin guiwa ne kan babban zabe na 2027.
Shugaba Tinubu ya kare gyara da a ka yi ga dokar zabe ta 2023, ya na mai caccakar ‘yan adawa da cewa ba daidai ba ne su yi korafin kan gyaran
Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana a Abuja Nasiru Adamu El-Hikaya Yana dauke da cikekken rahoto


