Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas
Published: March 19, 2026 at 3:41 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: March 19, 2026

Babban hafsan tsaron Najeriya, Olufemi Oluyede, ya bukaci al’ummomin jihohin Borno da Yobe da su kasance dasu ake yaƙi da ta’addanci, yana mai cewa hadin kai da goyon bayan jama’a na da matukar muhimmanci wajen kawo karshen rikicin.

Oluyede ya bayyana haka ne bayan tantance ayyukan rundunar sojin Najeriya kan yaki da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Ya ce binciken ya nuna cewa nasarar ayyukan soja na da alaka kai tsaye da irin hadin kan da ake samu daga al’ummomin yankin. Ya kuma yi gargadin cewa ta’addanci ba zai yi karfi ba sai da taimakon wasu daga cikin jama’a.

A cewarsa, wasu rahotanni sun nuna cewa akwai mutanen da ke taimakawa ko boye ‘yan ta’adda, abin da ke kawo cikas ga kokarin sojoji tare da tsawaita wahalar da jama’a ke ciki.

Ya kara da cewa galibin masu aikata laifukan ba baki ba ne, illa mutanen da ake sani a cikin al’umma, ciki har da makwabta da ‘yan uwa.

Don haka, ya bukaci jama’a su daina jin tsoro ko nuna bangaranci, su rika tona asirin masu laifi tare da hana su mafaka.

Oluyede ya jaddada cewa yaki da ta’addanci ba aikin soja kadai ba ne, illa aiki ne na kowa da kowa, yana kira ga jama’a su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.

Ya kuma bayar da misali da wani hari a Kukawa, inda aka gano wasu ‘yan ta’adda da suka ji rauni suna cikin al’umma, abin da ke nuna yiwuwar hadin baki.

Babban hafsan ya tabbatar da cewa rundunar soji na ci gaba da kokarin dakile sabbin dabarun ‘yan ta’adda, ciki har da amfani da jirage marasa matuki (drones).

Haka zalika, ya bukaci sarakunan gargajiya, malamai, matasa da kungiyoyin farar hula su kara taka rawa wajen wayar da kan jama’a da yakar tsattsauran ra’ayi.

A karshe, ya bukaci ‘yan kasa su kasance cikin shiri, su rika kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba, tare da tabbatar da cewa rundunar soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin Arewa maso Gabas.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Karamar Sallah: Hukumar Kashe Gobara A Gombe Ta Kuduri Aniyar Kare Al’umma
Next Post: Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas

Karin Labarai Masu Alaka

Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
Anyi Taho Mugama Tsakanin ‘Yan Sandan Turkiyya Da ‘Yan Kungiyar ISIS Afrika
Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
An Kama Maharan Bom Din Maiduguri Tsaro
Shugaban Kasar Najeriya Ya Gabatar Da Kudi Fiye Da Naira Triliyan 58 A Matsayin Kasafin 2026 Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
  • Sojin Ukraine Sun Janye Daga Gabashin Kasar Amurka
  • Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
  • Turkiyya Tana Gudanar Da Binciken Kasar Da Suka Kona Tutar Ta Tsaro
  • Kasar Saudiya Zatayi Gwajin Noman Dabino A Kano Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
  • NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.