Bangladesh ta sami rangwamen harajin da Amurka ta aza mata zuwa kashi 19 cikin dari, karkashin wata yarjejeniyar cinikayya da kasashen biyu suka rattabawa hannu ranar Litinin, wanda ya dauke haraji kan wasu sutura da aka hada da kayayyaki daga Amurka.
Shugaban gwamnatin Bangladesh na wucin gadi Mohammed Yunis, yace Amurka ta amince a bullo da tsarin ta yadda wasu suturu da aka dinka daga Bangladesh tare da amfani da auduga daga Amurka da wasu kayayyaki, ba za’a aza musu haraji ko na sisin kobo ba idan aka shigo da su kasuwannin Amurka.
Fadar White Huse tace Bangladesh ta amince zata baiwa kayayyaki daga masana’antu da albarkatun gona da zasu hada da nama, kaji da madara daga Amurka ciki harda motoci da dai sauransu fifiko a kasuwannain ta.
Yarjejeniyar ta kuma nuna cewa Bangladesh tana shirin sayen jiragen sama kirar Boieng 14 tana kuma iya karawa kan wannan adadi, kamar yadda bayanai daga ofishin babban jami’in cinikayya na Amurka suka nuna.


